album cover
Jininmu Ya Haddasa Kauna
1,335
Dance
Jininmu Ya Haddasa Kauna was released on May 3, 2018 by Apple Media Africa as a part of the album Iconic Sounds of Africa, Vol. 2
album cover
Release DateMay 3, 2018
LabelApple Media Africa
Melodicness
Acousticness
Valence
Danceability
Energy
BPM89

Music Video

Music Video

Lyrics

Jininmu ya haddasa 'kauna harta samu guri a kalbi na
Sabo da abar so yasani ina ta zubar da kwalla
Jininmu ya hadda sa 'kauna naki na baka guri a kalbina
Akwai wanda nake so ba kai ba ka daina zubar da kwalla
Ku tayani, ku taimake ni na fada garari da waige
Gashi kauna tai juyi yanzu gashi ina ta hange
Wacce nake so ta guje ni, gefe tayi ajeni jibge
A garin son ba sukuni kullum sai zubar da kwalla
Jininmu ya hadda sa 'kauna naki na baka guri a kalbina
Sabo da abar so yasani ina ta zubar da kwalla
Gani na fada a tarko ban san sanda akai hakan ba
Ka sani ina danuwa kauna dakai bazan iya ba
Na fada ma zuciyata baza tai ma marhaban ba
Kasa bana sukuni fuskar ka ido ya kalla
Yau tinani ya ishe ni na rame a saboda kauna
Zuciyata ta aminta, dake take so zata zauna
Gashi so yayi mini daurin da bai bari a sarke raina
Mai laifi in na nifoki so za mu 'kulla
Jininmu ya hadda sa 'kauna naki na baka guri a 'kalbina
Akwai wanda nake so ba kai ba ka daina zubar da kwalla
Jininmu ya haddasa 'kauna harta samu guri a 'kalbi na
Sabo da abar so yasani ina ta zubar da kwalla
Ka sani so ba ayi mar dashi a inda bazai tsiro ba
Wanda yayi haka yayi nadama domin ba zai nasara ba
Toh idan hakane kaima bai kamata kai jira ba
Kanka ka sanya a tarko kullum kana zubar da kwalla
So a zuciya in ya zauna dukkan sukuni yake hanawa
Na sakaki cikin kalbi ke kuma kina gujewa
Nayi saka nayi tubka, ya kike son warwarewa
Ki taimakeni ki agajeni na samu hanyata ta 'bulla
Jininmu ya haddasa 'kauna harta samu guri a 'kalbina
Sabo da abar so yasani ina ta zubar da kwalla
Eh ni zabina na nuna, bazan yi masa yaudara ba
In nama so karya gaba dani zakayi gaba
Kaima mutu sai ka nema nasan bazaka rasa ba
In 'yar birni kakeso, ka bincika tsakiyarmu dala
Jininmu ya haddasa 'kauna harta samu guri a 'kalbina
Sabo da abar so yasani ina ta zubar da kwalla
Jininmu ya hadda sa 'kauna naki na baka guri a 'kalbina
Akwai vwanda nake so ba kai ba ka daina zubar da 'kwalla
Written by: Nura Musa Inuwa
instagramSharePathic_arrow_out􀆄 copy􀐅􀋲

Loading...