Lyrics
Eh Allah sarki Duniya abin cikinta nake kalla
Ihsan taso taso miye yakeyin damunki
Damuwa ki rike daure idanuwanki subar 'kwalla
Komai baiman dadi a duniyar da nake zaune
Lamaringa da na kalla abin yana 'konan raina
Yau ni Ihsan malam a dole ne nayo 'kwalla
Yanayi yai sauyawa yau da gobe ta Allah
Zaman Duniya a kullun mai hakuri shike yo dace
Ga wasu nan na wanawa da lafiya wasu na nan kwance
Yayin da wani ke darawa a lokacin wani ke 'kwalla
Eh tamkar nima da ba abinda zan iyawa kaina
Yanayina dubeshi ba kafar yawo guna
Har so nacikin rai babu maiyiman sai ummi na
Rana zafi inuwa 'kuna ni ayau wazan kalla
Eh Allah sarki Duniya abin cikinta nake kalla
Ihsan taso taso miye yakeyin damunki
Yau ni Ihsan malam a dole ne nayo 'kwalla
Eh ihsan ni ki saurara gareki zanyi tunatarwa
A gurin Allah sarki kizamma maiyin godewa
Shi yayo ki yayo kowa domin nufin wa'azantarwa
Ba banbanci ne ba damu dake daya ne jimla
Komai baiman dadi a duniyar da nake zaune
Lamaringa da na kalla abin yana 'konan raina
Yau ni Ihsan malam a dole ne nayo 'kwalla
Eh Allah sarki Duniya abin cikinta nake kalla
Ihsan taso taso miye yakeyin damunki
Damuwa ki rike daure idanuwanki subar 'kwalla
Eh a sa'o'ina nice daban kagansu suna wasa
Wannan ya tabo wannan fagen gudu wasu na gasa
Duk yadda naso na bisu ba yadda zanyi na lumfasa
Dan kallan su bani sanin sa'in da nake 'kwalla
Umm baiwar Allah gareki lallai gaban ki Ihsan ta safka
A cikin jama'a ki gane sudai irinki basuda tamka
Kiran da nake gunki idanuwanki subar kuka
Rayuwarki ki saurara kyayi gani ikon Allah
Eh Komai baiman dadi a duniyar da nake zaune
Lamaringa da na kalla abin yana 'konan raina
Damuwa ki rike daure idanuwanki subar 'kwalla
Lamarina kowanne ga Rabbana na mika shi
Dan shine mai Komai shi zai nufeni na dau dashi
Da salatin manzon sa Aminu mai dadin 'kamshi
Shi zana rike wata rana nima nazama abin kalla
Eh Allah sarki Duniya abin cikinta nake kalla
Ihsan taso taso miye yakeyin damunki
Damuwa ki rike daure idanuwanki subar 'kwalla
Eh Komai baiman dadi a duniyar da nake zaune
Lamaringa da na kalla abin yana 'konan raina
Yau ni Ihsan malam a dole ne nayo 'kwalla
Written by: Nura M. Inuwa