Credits
Lyrics
Ehh dan yanxu dake na saba wata rana sai labari
Dan kinyi daban da uwar mugu ke zana rike ki dube ni
Nasan lamarin soyayya wata rana sai labari
Indai kazamo uban 'ya 'yana zanyi daban da uwar mugu
Hee so ya hana natsuwa guna ya zanayi na shige tarko
Na amsa zanyi soyayya to kaina zaya 'dau iko
Ki amince mani in turo gidan ku azo ayi baiko
Kizamma uwar 'ya 'yana nasan na kece raini
Nasan lamarin soyayya
Wata rana sai labari
Dan kinyi daban da uwar mugu
Ke zani rike ki dube ni
Fili na tsaya ina duba a mazaje wa zan 'dauka
Banaso inyi ruwa na ido daga 'karshe sai na hango ka
Kallon kallo muke da ido ga zuciya na tayin duka
Haba tsoro ln me kake na ido inna juyo zo ka kalleni
Yanxu dake nasaba wata rana sai labari
Indai kazamo uban 'ya 'yana zanyi daban da uwar mugu
Eh so 'kauna ne ya kawo ni aure zamuyi idan kin shirya
Ni na shedan ki zancen nan kallanki nake da kyan niyya
Kan tsari zanai taku har inyi rawa in juya
Daga karshe karkiyi man halin matan zamani
Nasan lamarin soyayya
Wata rana sai labari
Dan kinyi daban da uwar mugu
Ke zani rike ki dube ni
Eh nasaka cikin rai kuma sannan ka zauna 'kalbina
Ba ja kuma sannan babu gudu ko taro kai zan nuna
Kai 'dinga farin masoyi ne buri munyi auren sunna
Kibiyar 'kauna ka harbo tazo kuma ta sameni
Hee wani albishir zana maki dubeni da 'dan farin goro
Tashin muryarki nake so mai dadin ji har da sauraro
Kinsan haka koko a'a magana ce bana 'kwauro
Ya sarewa murya taki dan dadi ta birgeni
Nasan lamarin soyayya
Wata rana sai labari
Dan kinyi daban da uwar mugu
Ke zani rike ki dube ni
Ye in kayi ado ya 'dawisu maza rakiya sukan yima
Tuni naga zabe namiji kaine reshen dana kama
In nayi kiranka my only amsa bana dadin kalma
Bisa yarda nina karbeka ga hannu nawu kajani
Eh dan yanxu dake na saba wata rana sai labari
Dan kinyi daban da uwar mugu ke zana rike ki dube ni
Nasan lamarin soyayya wata rana sai labari
Indai kazamo uban 'ya 'yana zanyi daban da uwar mugu
Written by: Nura M. Inuwa