Lyrics
Minal a so kin batar da zuciya ta mace
Ki tausaya karki sani bangare na yaudara
Ina gudun duniya
A duniya inka barni babu inda zan shige
Sunan Minal yafi kyau a gunka ko wajen kira
Kabar ni ya zanyi ne?
Daso da kauna suna a tare duba tafiya
Kamar Minal ne da sahibinta zara ga wata
Sun haskake duniya
Eh cikin mafarkin danayi jiya naga ka mace
Da kafito in naganka kanna farga ka bace
Daure masoyi karka maisheni tushiyar sanka ce
In babu kai ni ina a raye
Gawa da rai nake
Cikin zaman duniya
Daso da kauna suna a tare duba tafiya
Kamar Minal ne da sahibinta zara ga wata
Sun haskake duniya
Baki rufe kedai Minal daina yin kiran mutuwa
Ki kaddara sai lokaci yayi zamu yo rabuwa
Dani dake yau mun kasance aboka nan rayuwa
Da mun fito tare rana gashin ki keyi min inuwa
Idan kina walkiya
Daso da kauna suna a tare duba tafiya
Kamar Minal ne da sahibinta zara ga wata
Sun haskake duniya
Kai durkusawa chan saman bayanka nina haye
Uwa uba karshen a so gurbin sune ka maye
Ka rage zance in ba dani ba Tunda dai na tsaye
Wayyo ni Allah mutuwa kanka zatabar kewaye
Ganin ka san zuciya
Daso da kauna suna a tare duba tafiya
Kamar Minal ne da sahibinta zara ga wata
Sun haskake duniya
Daso da kauna suna a tare duba tafiya
Kamar Minal ne da sahibinta zara ga wata
Sun haskake duniya
Me zan da kaina inba Minal ni ganin ki shi nafi so
Da lafiyar ki sanan da rai naga inda zan karaso
Kece guda zan nufo gareki kofa buden dana kwankwaso
Zuwa da kai ya zarce sako
Inba kiso mai iso
Sanunki zinariya
Daso da kauna suna a tare duba tafiya
Kamar Minal ne da sahibinta zara ga wata
Sun haskake duniya
Minal aso kin batar da zuciya ta mace
Ki tausaya karki sani bangare na yaudara
Ina gudun duniya
A duniya inka barni babu inda zan shige
Sunan Minal yafi kyau a gunka ko wajen kira
Written by: Nura M. Inuwa