album cover
Madina
164
World
Madina was released on January 17, 2019 by Apple Media Africa as a part of the album Iconic Sounds Of Africa, Vol. 3
album cover
Release DateJanuary 17, 2019
LabelApple Media Africa
Melodicness
Acousticness
Valence
Danceability
Energy
BPM100

Music Video

Music Video

Lyrics

Eh lokaci yayi inda rai da rabo
Madina kin dawo, ba kinyi nesa dani
Madina tun farko ke nake ra'ayi
Idan da rai da rabo karka yada ni
Mutum yana tare da abinda yake so
Shi rabon kwado bazaya hau sama ba
Eh zuciya nazari aikin ta ne zance
Afuwa ko zaba daka zans tantance
Dan rashin ki Madina idanu suka 'kankance
Kamarki nai hange bazani samu ba
Mutum yana tare da abinda yake so
Shi rabon kwado bazaya hau sama ba
Eh kalma taso ga mutum 'daya ne wani ba'wa rance
Mallakar abin so da zuciya kaga ai shine dace
Gari na masoyi baya nisa ai hakika ce
Nesa gata a kusa dani banyo zaton haka ba
Mutum yana tare da abinda yake so
Shi rabon kwado bazaya hau sama ba
Eh allurai dake a cikin ruwa mai rabo shi yake tsinta
Nai gamo nakatar nai tsintuwar adalar mata
Ta mallakan zuciyar ta a hannu ta sakan zoben ta
Rashi na wannan 'ya bazana so nai ba
Mutum yana tare da abinda yake so
Shi rabon kwado bazaya hau sama ba
Mutum yana tare da abinda yake so
Shi rabon kwado bazaya hau sama ba
Dukka mai nazari lamarinsa shi yake dacewa
So da kamar wasa a hankali ake farawa
Wataran mu zame 'daya nida kai har mu sabawa
Rukon amanata Allah sa baka gujen ba
Mutum yana tare da abinda yake so
Shi rabon kwado bazaya hau sama ba
Eh wata rana ce nake ta jiranta tazaowa
Sanadi na rashinki Madina na kusan zaucewa
Na cire soyayya zuciya taki yarjewa
Mai hakuri roman dutse bazai wuce sha nasa ba
Mutum yana tare da abinda yake so
Shi rabon kwado bazaya hau sama ba
Ga amanar kaina ka rike karka kasawa
Muyi zaman mu na aure nida kai muyi 'daurewa
Tinda juna namu munaso anyi shedawa
Innama laifi 'karami kadda kai duba
Mutum yana tare da abinda yake so
Shi rabon kwado bazaya hau sama ba
Eh lokaci yayi inda rai da rabo
Madina kin dawo, da kinyi nesa dani
Madina tun farko ke nake ra'ayi
Idan da rai da rabo karka yada ni
Mutum yana tare da abinda yake so
Shi rabon kwado bazaya hau sama ba
Written by: Nura M. Inuwa
instagramSharePathic_arrow_out􀆄 copy􀐅􀋲

Loading...