Music Video

Murmushi
Watch {trackName} music video by {artistName}

Credits

PERFORMING ARTISTS
Isah Ayagi
Isah Ayagi
Performer
COMPOSITION & LYRICS
Isah Ayagi
Isah Ayagi
Songwriter

Lyrics

(Mai atamafa on the beat) Koda ina yanayin fushi in na gan ki ina jin natsuwa Tare muke kashe damuwa haka tare muke gina murmushi Wanda ya kasa tare fushi ko cikin mata shine rago So ne kogin damuwa san da zaka wuce wani zai shigo Tsintar allurar ruwa sai rago yin dambe da bahago Jin kwarin gwiwa a kaunar ki shi ya dada min karsashi Fuska ta ko takan kasance kamar nono a cikin fura Kullum a cikin murmushi ido baya haduwa da gira Kuna babu a zuciyata ko sanyi yafi na kankara Wani zai bata mini zai wuya kuga nayi saurin fushi Majalisa ta koda yaushe da zance naki nake bari Maudu'i na kan kasance akan lafazin ki ya tattari Mai kushe ki da na tsaya jin sa gwara bakin haushin kare Nifa akan a taba ki har gwanda nayi tafiya kan garwashi Ko yaushe a cikin mafarki nakan tashi da fuka-fuki Nayi sama har inje gurin da taurari ke shan hantsaki In nuna masu ke su shaida da tsananin son da nake miki Har watarana sukan rakoni na gan ki na kare da murmushi Tunda na fara ado da kaunar ki bani zama ba kwalliya Kullum burina na birge ki babu dare ba safiya (ba safiya) Na shirya tsaf don na aure ki ga bunjima da tagiya Shiko sadaki ko kudin ajiyar kurma zan bada shi Hayya Hayya-hayya-hayya Hayya-hayya Ke da rashin ki ko gwara yama ce ga sama zata rikirkito Gara ace kura ta balle tazo muyi fito na fito Dana rasa ki ko gwanda na fada maliya ba jirgin fito In na rasa ki kahon kiyama idan yana guna zan busa shi
Writer(s): Isah Ayagi Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out