album cover
Double 4
4,296
Blues
Double 4 was released on February 2, 2020 by Sarkin Waka Musical Studio as a part of the album Ana Tayi Muna Taji
album cover
Release DateFebruary 2, 2020
LabelSarkin Waka Musical Studio
Melodicness
Acousticness
Valence
Danceability
Energy
BPM117

Credits

PERFORMING ARTISTS
Nazir M Ahmad Sarkin Waka
Nazir M Ahmad Sarkin Waka
Performer
COMPOSITION & LYRICS
Nazir M. Ahmad
Nazir M. Ahmad
Songwriter

Lyrics

[Verse 1]
Baba a rushe (Baba a rushe)
Baba a gyara (Baba a gyara)
Baba a rushe (Baba a rushe)
Baba a gyara (Baba a gyara)
[Verse 2]
Mu baba a gyara, baba a rushe mana mun bi
Baba a rushe mana mun bi
Mu baba a gyara yafi
Maza Baba ka gyara mana yafi
Malam Nasiru El'rufa'i guduma mai fasa karya
[Verse 3]
Yanzu Kadunan da aka yi dace maza kai je ka ka nema
Malam Nasiru El'rufa'i guduma mai fasa karya
Tun daga aikin Sardauna ba a aiki sai san da ya dawo
Malam Nasiru El'rufa'i guduma mai fasa karya
Kai bana na ga sun moru da tukin nan motar sun samu kwararre
Malam Nasiru El'rufa'i guduma mai fasa karya
Sai aikin ake musu na ji mutane ma na son maimai
Malam Nasiru El'rufa'i guduma mai fasa karya
Da duk zaki ya hadu da aiki to aikin sunanshi gamamme
Malam Nasiru El'rufa'i guduma mai fasa karya
[Verse 4]
Ashe 'yan Kaduna anai musu aiki su bana dai sun samu nutsattse
Malam Nasiru El'rufa'i guduma mai fasa karya
Ana yakin anai musu aikin kai lallai an kammala komai
Malam Nasiru El'rufa'i guduma mai fasa karya
Ana tafiya komai bisa aniya shi mashin ya dan dara keke
Malam Nasiru El'rufa'i guduma mai fasa karya
Fannin ilimi ma kaf a Arewa su nasun ya dau yin daidai
[Verse 5]
Malam Nasiru El'rufa'i guduma mai fasa karya
Fannin lafiya ana hirarka ashe kai Malam ka tafi daidai
Malam Nasiru El'rufa'i guduma mai fasa karya
Ai su Zaria ruwan da ya kai musu nan malam ya gama musu komai
Malam Nasiru El'rufa'i guduma mai fasa karya
Baban Bello baban Bashiru turmin nan da ake daka komai
Malam Nasiru El'rufa'i guduma mai fasa karya
Ku duba zarensu ta fannin tsaronsu ashe gwamnan suka ba wa kwararre
Malam Nasiru El'rufa'i guduma mai fasa karya
[Verse 6]
Ku duba shigarsu ta fannin diyansu ashe yunwa ba ta musu komai
Malam Nasiru El'rufa'i guduma mai fasa karya
Fannin gine-gine ana hanyoyi da ko jirgi sai ya bi a daidai
Malam Nasiru El'rufa'i guduma mai fasa karya
Fannin ilimi an yi masa tsarin da ko jaki zai samu kaso nai
Malam Nasiru El'rufa'i guduma mai fasa karya
Fannin lafiya an yi masa turken da ko gaba ma ba mai masa komai
Malam Nasiru El'rufa'i guduma mai fasa karya
[Verse 7]
Sannan tsarin kashe kudinsu ashe duk kasa shi ne aka koya
Malam Nasiru El'rufa'i guduma mai fasa karya
Kuma ma tsarin treasury single account nan ta Kaduna ya zo
Malam Nasiru El'rufa'i guduma mai fasa karya
Ai ni a sani na a nan aka fara ga shi a yau a kasa an dauko
Malam Nasiru El'rufa'i guduma mai fasa karya
Bala Bantex deputy gwamnan nan ni a sani na ya hada komai
Malam Nasiru El'rufa'i guduma mai fasa karya
A tambayi Abdu Kwari tsarin nan da su aka zauna an ka yi komai
[Verse 8]
Malam Nasiru El'rufa'i guduma mai fasa karya
Ku tambayi AG Umar Wazir da su tsarin nan ya tafi daidai
Malam Nasiru El'rufa'i guduma mai fasa karya
Ku tambayi SA Uba Sani shi tun a siyasa yag gama komai
Malam Nasiru El'rufa'i guduma mai fasa karya
Ku ce SSG gumbar dutse Balarabe Abbas bai mana karya
Malam Nasiru El'rufa'i guduma mai fasa karya
Da chief of staff Bashiru Sa'idu ashe bana karfe zai kuma kara
[Verse 9]
Malam Nasiru El'rufa'i guduma mai fasa karya
Hadiza Bala na ce muku MD Port Authority tai komai
Malam Nasiru El'rufa'i guduma mai fasa karya
Ina Janare da Bappa a je a ce wa matasa kar su yi sanya
Malam Nasiru El'rufa'i guduma mai fasa karya
Ka je Usmanu shagon waka kace ma mawaka su yi mi shi komai
Malam Nasiru El'rufa'i guduma mai fasa karya
[Verse 10]
Ko ni nan sarkin waka ma Naziru kida na ya fadi komai
Malam Nasiru El'rufa'i guduma mai fasa karya
[Verse 11]
Baba a rushe, Baba a rushe
Baba a gyara, Baba a gyara
Mu baba a gyara (Baba a rushe mana mun bi)
Baba a rushe mana mun bi
Mu baba a gyara mana ya fi
Maza baba ka gyara mana ya fi
Malam Nasiru El'rufa'i guduma mai fasa karya
[Verse 12]
Malam double 4
Ka yi rawa malam (4 ga 4)
Eh shi ne double 4
Ashe! yanzu ne fa muke son malam
Ya kara yin double 4 Kaduna
[Verse 13]
Kai dama-dama (Dama)
Dama gwamnan yai hudu (Yai hudu)
Sai ya kara yin hudu (Yai hudu)
In ya kai kuma yai hudu (Yai hudu)
Hudu sau hudu shi ne double 4 Kaduna
[Verse 14]
Malam double 4
Ka yi rawa malam (4 ga 4)
Ehhh shi ne double 4
Ashe! yanzu ne fa muke son malam
Ya kara yin double 4 Kaduna
[Verse 15]
Kai dama-dama (Dama)
Dama Buharin yai hudu (Yai hudu)
Sai yai karin hudu (Yai hudu)
In ya kara kuma yai hudu (Yai hudu)
Yai hudu sau hudu (Sau hudu)
Buhari hudu sau hudu
Malam Nasirun hudu sau hudu Kaduna
[Verse 16]
Sai ka yi double 4 kar ka matsa malam
4 ga 4 shi ne double 4
Ashe yanzu ne fa muke son Malam
Ya kara yin double 4 Kaduna
[Verse 17]
Waka waka ce (Eh) wata wakar sata ce (Kaduna)
Gemu gemu ne (Eh) wani gemun iska ne (Kaduna)
Aiki aiki ne (Eh) wani aika-aika ne (Kaduna)
Sanata sanata ne (Eh) wasu sanatan sata ne (Da sake)
Gwamna gwamna ne (Eh) wani gwamnan fosta ne (Kula fa)
[Verse 18]
Namun malam ne, don shi ne gwamna ma Kaduna
Malam double 4
Ka ji kidan malam (4 ga 4)
Ehhh shi ne double 4
Ashe yanzu ne fa muke son malam
Ya kara yin double 4 Kaduna
Malam double 4
Uban gidan malam (4 ga 4)
Kaduna shi ne double 4
Ku ce yanzu ne fa muke son malam
[Verse 19]
Ya kara yin double 4 Kaduna
Bara in gai da ciyaman na tsaruka double 4
Eh! don da shi an ka yi 4 Kaduna
Za a kuma kuma ai 4 eh
Shi yace mu yi waken Kaduna
Umar Waziri accountant genaral dan Kaduna
Allah Ya sa mu dace, Amin
Written by: Nazir M. Ahmad
instagramSharePathic_arrow_out􀆄 copy􀐅􀋲

Loading...