Lyrics
It's sd on the mix
Ba tsaro kasar bamu ma da yanci
Me yasa arewa ne ake zalinci
Hakane wasu babu gun makwanci
Talakawa na bukatar ayi masu adalci
Anbi abokina har hidansu an kashe shi
Na je zan gudu a hanya kidnappers sun tareni
A Nigeria watakalar rayuwa ake yi hanyoyin da basu billewa yanzu wai su ake bi
I am tired of this democratic bull shit
Abu ba lalle ba amma ana mata kunshi
Sun sa mu cikin kunci
Abu ba igiya ba ana yi mata kulli
No be say I no get ego
Magana nake a yau cike da damuwa
Daka fita akama ka a kira yan uwa
Ace dasu kudi ko ko ka rasa rayuwa
Nasan kun sani ayaunzu mi ke faruwa
A karato ma Nigeria nasi zuwa bakara
Shinkafa sai mai azziki marar shi sai dai masara
Zamuyi magana
Suna cewa kar mu fada, idan ba mai son mu ba waye zai daukaka talaka
Nazo na bayyana yanda nake ganin abubuwa
Taron dangi doesn't really mean tururuwa
In dai baka tabattar ba kar ka hau rahoto
Haram, yanzu ake hadawa da boko
Kar ku ce fulani ba dan adam bane
Ana kona masu ruga wai ba yan kasar bane
Ana kashe su a kudu duk kasar mu ne
Damuwar su name haka yan uwanmu ne
What this **** up to
So disrespectfull
Alhamdulillahi I am very very grateful
It's like you don't even know what we're going through
Corona, lasa ebola yanzu bedflu
Duk mu kadai, ku daga mana kafa mana
Haba mana, ku bar Nigeria ta cigaba mana
Allah baza mu iya ba, toh ka iya mana
Gara mulkin da dana yanzu mana
Ai da bamu magana yanzu an tabo mu
Mawaka yanzu mun zo ku bada gudunmuwamu
Laifin wani bai kamata ya shafi wani ba
Haba manyan mu ya kamata ku dinga tausai
Tunda kowa dai yana bukatan dausai
Hah, la'akari da tsautsayi
Wahala, laulayi Allah dai ya tsare mu daga wani tsautsayi
Zantuka nake tayi cike da kafiya
Mu fulani an sanmu muna da yafiya
Duk da ba'a tabamu a zauna lafiya
Gwamnati a gyara dan azauna lafiya
Eh, mu yan arewa ne
Gwamnati ku duba mu
Written by: Umar Alhassan Dalhatu