album cover
Mamah
14,516
Pop
Mamah was released on May 25, 2018 by White House as a part of the album Sabon Salo
album cover
Release DateMay 25, 2018
LabelWhite House
Melodicness
Acousticness
Valence
Danceability
Energy
BPM100

Music Video

Music Video

Credits

PERFORMING ARTISTS
Adam. A. Zango
Adam. A. Zango
Performer
COMPOSITION & LYRICS
Adam. A. Zango
Adam. A. Zango
Songwriter

Lyrics

Mama ayye ayye
Mama ayye ayye
Mama wayyo
Mama iye
Mama uhmm
Mama oh oh
Mama
Kin rikirkita min tunani na
Kai son ki ya shiga قلبي na
Mama yee Mama yee
Ya Mama hasken rayi na
Mama yee Mama yee
Mama kifi guda a cikin rafi
Mama yee Mama yee
Mama kaunar ki ta shiga ruhi na
Mama ayye ayye
Mama ayye ayye
Mama wayyo
Mama iye
Mama uhmm
Mama oh oh
Mama
Kai mabiyan duka waka ta
Kara sauti kan murayar ka
Wata rana a daki na
Ina a kwance katifa na
Amo nake ji na tashi
Ashe kara ne na waya na
Sai na firgita na tashi
Na farka bacci na zauna
Sai nace waye wannan
Yake ta faman damu na
Sai na dauka na duba
Ba number kuma ba suna
Na chanza fuska nayi tsaki
Na kara jawo bargo na
Nan na koma na kwanta
Don bacci ne a idanuna
Na riga na sha aiki
Ga gajiya a gabobi na
Sai na sake jin sabon kara
Yana ta kuskure kunne na
Mama yee Mama yee
Ya mama hasken rayi na
Mama yee Mama yee
Mama kifi guda a cikin rafi
Mama yee Mama yee
Mama kaunar ki ta shiga ruhi na
Ku tsaya kuji dan gina
Shin wai wake damuna
Baya ko jin tausayi na
Don ya hana inyi bacci na
Na duba kuma ba suna
Yana shiga mini hakki na
Mama yee Mama yee
Saina dau waya ta na danna
Sannan na kara a kunne na (Hello)
Sallama bisa tsarina
Shin wai wake damu na?
Sai tace "Adam Zango"
"Wa'alaika masoyina"
"Abin tunanin ruhi na"
"Ai yanzu zaka ji suna na"
Sai tace "Nice mama"
"Yanzu zaka ji sirri na"
Mama yee Mama yee
Ya mama hasken rayi na
Mama yee Mama yee
Mama kifi guda a cikin rafi
Mama yee Mama yee
Mama kaunar ki ta shiga ruhi na
Mama yee mama yee
Kin rikir kita min tunani na
Kai son ki ya shiga قلبي na
Mama yee Mama yee
Ya mama hasken rayi na
Mama yee Mama yee
Mama kifi guda a cikin rafi
Mama yee Mama yee
Mama kaunar ki ta shiga ruhi na
Mamaye mamaye
Saboda dadin muryarta
Saina goge idanuna
Nayi godiya gun Allah na
Don naji ta fadi sunana
Mamaye Mamaye
Sai tace "Adam Zango, nima halittar Allah ce"
"Ba kamar ka ba mai sona"
Sai nace "baiwar Allah, mai kike nema guna?"
"Waya baki fa lamba na"
"Kika kasa kiran rana"
"Sai cikin dare kika damu na"
Mamaye mamaye
Sai tace "Adam zango"
"Zan bayyana maka siffa na"
"Kar ka tsorata mai sona"
"A hankali kaga hali na"
Mama yee mama yee
"Ni aljana ce ba shakka"
"Amma ina da tsoron Allah na"
Sai na firgita dangina
Na kauda wayar a kunne na
Bacci na sai ya kare
Sai sake sake a ruhi na
Sai nace "wayyo Allah, nayi gamo fa a harka na"
Mama yee Mama yee
Ya mama hasken rayi na
Mamaye Mamaye
Mama kifi guda a cikin rafi
Mama yee Mama yee
Mama kaunarki ta shiga ruhi na
Mama yee mama yee
Harkar mutum ya sha kaina
Ga aljanu kuma na bina
Na kosa gari ma ya waye
Dan in sanar da iyaye na
Mamaye mamaye
Da gari yayo haske
Nayi sallar asbahi na
Al'ajabi kuji dangina
Na kasa karya kumallo na
Ga yunwa na damuna
Na kosa inga Umma na
Mai share mun kuka na
In fada mata sirri na
Domin ta share hawaye na
Mamaye mamaye
Nai wanka kuma na shirya
Na dau jakar computer na
Na dau mukkulin mota na
Sannan na kulle dakina
Mama mama (wayyo)
Naje na shiga mota na
Da sake sake a rayina
Ina ta tukin mota na
Na rasa me ke damuna
Mama mama (wayyo)
Na kunna sautin mota na
Domin ya debe kewa na
Sai naji ance" zango" cikin sifikun mota na
Mama Mama
Nai maza na taba burkina
Jin muryan a kunne na
Sai tace "nice mama"
"Karda ka tsorata mai sona"
Mamaye Mamaye
Tace "albishirin ka fa zango na"
"Na zarce kowa sonka"
"Da tausayin ka a ruhina"
Saita bayyan siffar ta
Gata zaune a gefe na
Uhmm wayyo kaina
Kyakkyawa kuji dangina
Ina ma ku gane kwatance na
Naso na bayyana kyawunta
Amma ya zarce tunani na
Mamaye mamaye
Sai tace "kaji zango na"
"Kar kayi mamaki na"
"Ni yar sarkin Aljan"
"Baba na kuma na sona"
"Ni da kai Adam zango"
"Muna nan tare cikin kauna"
"Zana barka fa zan koma"
"Ba zaka sake gani na ba"
"Sai dai ka dinga tunanina"
Mamaye mamaye
Sai ta bace daga fuskata
Ina nan zaune a mota na
Amma kaunar ta ya shiga ruhi na
Mamaye mamaye
Allah aljana yau tashiga ruhi na
Mamaye mamaye
Kin rikir kita mun tunani na
Kai son ki ya shiga قلبي na
Mama yee Mama yee
Ya mama hasken rayi na
Mama yee Mama yee
Mama kifi guda a cikin rafi
Mama yee Mama yee
Mama kaunar ki ta shiga ruhi na
Written by: Adam. A. Zango
instagramSharePathic_arrow_out􀆄 copy􀐅􀋲

Loading...