Music Video
Music Video
Credits
PERFORMING ARTISTS
Auta Mg Boy
Performer
COMPOSITION & LYRICS
Abdulrahman Muhammad Garba
Composer
Lyrics
Uhm-mm-mm-mm
Lala-lala-lala
Eh kaine farin cikin raina
Kai nake kauna
Dana sani ashe keya ce
Daure ka yafe min
Kullum idan ina zaune
To kai nake zance
Na kasa gane meke damuna
Duk na susuce
Na sake reshe na rike ganye
Gashi nai kwance
Shi wanda nafi bawa amana
So da yayai kwace
Na kasa gane mai kaunata
Sai yanzun na tantance
Duka hada da zagi gunsa
A dare zuwa rana
Eh nai dana sanin
Soyayya da waninka ban dace ba
Samun nasara
Hakuri tushen ta ba zance ba
Zan iya mutuwa hakuri
In har ka fada baza kayi min ba
Nidai kuskuren afuwa kai min
Bazai rage komai ba
Dana sani keya
Duk wanda yayi ta ba daga nan ba
Ya mai martaba
Yafe min laifin da nai na tuba
Eh so nayi mai shigar sauri
Amma garan yayo tsauri
Na fasa inyi mai tsari
Yau gashi banji dadi ba
Dana sani nayo farko
Ni kuskuren sa na dauko
Yau gani babu mai ikon
Shi so da yayai min danba
Kai afuwa garan yafi
Dan so ya daina min zafi
Inka ki sai nai dawafi
In roki rabbana sarkin mu
Kin tsane ni babu dalili
Ban san me uzurin ki ba
Na soki babu misali
Amma ke bayki ganshi ba
Na roke ki iya roko
Amma a so bayki ji shi ba
Duk wanda yaki ka a farko
To fa bazai taba sanka ba
Bazan yarda dake ba
So bazanyi na dole ba
Kinki min uzuri
Da fari sanki a raina na sakaba
Bazana koma ba rana
Da bai bulewa
Written by: Abdulrahman Muhammad Garba, Umar Big Show