album cover
Buri
7,604
Afro-Beat
Buri was released on October 10, 2022 by Sadiq Saleh Prod. Distri. By Mr. ArewaBlog as a part of the album So Kenan
album cover
Release DateOctober 10, 2022
LabelSadiq Saleh Prod. Distri. By Mr. ArewaBlog
Melodicness
Acousticness
Valence
Danceability
Energy
BPM120

Music Video

Music Video

Credits

COMPOSITION & LYRICS
Sadiq Saleh
Sadiq Saleh
Songwriter

Lyrics

[Intro]
Ay, zo cika burina
Ki shige ɗakina
In zama ango
Ke zamo matata
Tuntini na tsaida ka uban 'yaʼyana
Sha kurumunka kana a cikin ƙalbina
[Verse 1]
Zo ki ji ga wani saƙo za na fitar daga bakina
Nai ajiyar sa suna ta yi min yawo a gaɓoɓina
Ko shingiɗa na yi sai na ga kin zo min a mafarkina
Da baki zo ba kamar zan cuɗanya da ƙwaƙwalwana
Albishirinki ki ce goro ki yi sauraro
Son ki yai ma ni maruru har na warke ma ban yi aune ba
Ban yi aune ba
[Verse 2]
Eh, kai ajiya a cikin rai ba da shiri ba
Yadda na so ka ka so ni ka min ni maraba
Za ni kasa in tsare kan abin da zaɓa
Wacce ta raɓi abin da na so ta ga arba
Albishirinka ka ce goro
Ka yi sauraro
Ni da kai na yi tunƙaho
Duniya sun shaida kalamaina
Sun shaida kalamaina
[Verse 3]
Cutuwar da take cutar da ni, ha
A son ki ta san na cutu
Bautuwa da take bautar da ni, ha
A son ki ta san na bautu
ʼYantuwa ki taho ki yi lamuni, ha
Ni ma a gan ni na ʼyantu
[Verse 4]
So mahaɗi na
Dan yai mi ni rana
Kar kuji haushi in kun ga tai mi ni laifi
Ban ji ƙuna ba
Soyayya ce
[Verse 5]
A ka gan ni da kai ikon Allah ne, ikon Allah ne
Ni kam a gare ni dubun nasara ne, dubun nasara ne
Wanda ya ƙi hakan sai ido ya tsiyaye, ko wane ne
Fatan nasara ga dukkan ku magauta
Mun sha Tabara da Yaseen
[Verse 6]
Ina son ka
Son ka ya bi cikin ƙashina
Ina son sa
Ko ba a so ina san ka abina
[Outro]
Zo cika burina
Ki shige ɗakina
Sha kurumunka kana a cikin ƙalbina
Written by: Sadiq Saleh
instagramSharePathic_arrow_out􀆄 copy􀐅􀋲

Loading...