Lyrics
Zuci zan buda naji kamar tana duka
So ya harbe ta, inda yaja ta zan kai ta
Ba wanda yaki mai yin soyayya jure bakar wuya
Tamkar hatsari take in an fada dole a tausaya
Ba wanda yaki mai yin soyayya jure bakar wuya
Tamkar hatsari take in an fada dole a tausaya
An ce komai nisan jifa kasa yake dira
So ne zai canza min suffa, naki nake hara
Bango yayi tsirrai da yasa don sa na yunkura
Kinsan suka tayi sai da ruwa dole take tsira
Amsan kalmomi na ka aje dukka a zuciya
Dace koko rashi duk daya ne, an masu lokaci
Kalmomin da kamin rai ya nade zan maka tsokaci
Yarda zana sakar miki mu dade, bani da firgici
Zanje inda kaje duk mu hade, so da kwalafuci
Dama ke na zata wacce rabo zai hana shan wuya
Zai hana shan wuya
Lallai jan damara za na dada don na kula da kai
Komai zana fada babu rada tunda ina dake
Nasan dole jini na ya kada inko na yada kai
Tarkon so da yake karya gada shi muka tsallake
Hannu zamu hada a tare a san mun zama lubiya
Zo, zo, zo muje
Nima alkawari za nayi ma zan maka ladabi
Komai kika fada babu musu zana ji zana bi
Nuni in kayi min don na kula ban cire kallabi
Zana min adabin so na biya mai gina dalibi
Nuni zata fi kai zana raka kayi masoyiya
Eh kayi masoyiya
Kayi masoyiya
Written by: Ahmad Idris Abdulkarim


