album cover
Filin Daga
386
Afro-Pop
Filin Daga was released on August 11, 2023 by 4855157 Records DK as a part of the album Filin Daga - Single
album cover
Release DateAugust 11, 2023
Label4855157 Records DK
LanguageEnglish
Melodicness
Acousticness
Valence
Danceability
Energy
BPM136

Credits

COMPOSITION & LYRICS
Umar m lawal zamangaa
Umar m lawal zamangaa
Songwriter

Lyrics

Filin daga ah ha aa ah ah ah
(Zamanga)
Oh 'kauna tasani a filin daga
Soyayyar ku taiman rana
Al-'kawari na karda ku manta
Dan banso muyo bankwana
So ya jefa ni a filin daga
Soyayyar ka taiman rana
Al-'kawari na karda ka manta
Dan banso muyo bankwana
Eh da saurina na 'dau hanya
Domin zani gun soyayya
'Kananu na kaya na sanya
Na banbance safe da rana
Na dakko fure na ruko
Kasan jijiya na hako
Tulin igiya na cuko
Madaurin yawan zancena
Eh garin yayi kyau ga iska
Kadawa take san barka
Bukatata in kalleka
Cikin rai nabaka mazauna
Ruwan so jiki ya zubo
Ya wanke 'kasa da tabo
Idan har da rai da rabo
En yara baje maka yauna
Oh daso kinkayimani suka
Yasa har nazoni na tanka
Cikin zuci kinkayi saka
Kin 'daure jiki da ganina
Kalamanki sufi ruwa
Ki furta nataka rawa
Akan sanki ban tabuwa
Sai na doke duk na gabana
Eh kana kyau da furta harruffa
Da kaya a dole a tafa
Kazo zana shirya liyafa
Na nunaka gun yayyena
Hakika inada gwani
Nace naji nakwa gani
Biki zani bani zani
Burina kazamma mijina
Kowa ya lula cikin soyayya
Akan sanka zanyi biyayya
Dadi ko wuya na shirya
Ka turo a samana rana
Masoyan mu duk kufito
Magautan mu zasu mutu
Ha aa kibar furta wanga batu
To nai laddabi ga gwani na
Ah, ah, ah, ah
Ha aa aa ah
Filin daga
Mix by zamanga
Written by: UMAR M LAWAL
instagramSharePathic_arrow_out􀆄 copy􀐅􀋲

Loading...