Credits
COMPOSITION & LYRICS
abdulkadir tajuddeen
Songwriter
Lyrics
AD music studio
A tsakaninmu ni da ke
Ba rabuwa mun dace da juna
A tsakaninmu ni da kai
Ba rabuwa mun dace da juna
Laifin wani ai baya shafar wani
Bai dace ba fushin ki da fushin wani
So na hanan ganin laifi nasani
In kin manta dole nayi miki tuni
Rayuwa dake nakeso mu fara
In ba ke ba wa zan tunkara
Dawo taho mu gyara
Rabuwa bai dace da mu ba
'Yar uwata dole nayo kishin
Abinda kayo mata ba fashin
Komai kace dole nayi shi
Ko da zai zamo ajalin lumfashi
Hakuri jeka ka bata
In kuma ka ki bazamu dawo ba
Tun farko ita taja bani ba
Ni me nayi mata?
Ita burinta ni da ke mubar soyayya
Kin ga ta bata
Ta rikice sai tura sakonni take
Mi zan ce mata?
Na saurareta zatayi kuka
In kau na bita na bata harka
Maciya amana ce ki bat kallonta
Wallahi sam batayi dace dake ba
Ashe haka za muyi kawata
A zuciyarki ba so sai mugunta
Rigar mutuncina ce zaki keta
Shekara da shekaru kanta nake ta bauta
Sai da Allah ya bani zaki mini keta
Kama hanya ki barni dan nayi rayuwata
Dan nayi rayuwata
Haka zakije wani ba zai jiyo ba
Written by: abdulkadir tajuddeen

