Lyrics
Allah karimun ganiyun rahimu
Shi yayi dare jallah shi yayi rana
Yayai dan adam mai wuyan gane hali
Oh-oh bil adam mai wuyan gane hali
Wata ran mutum ai yakan munana ma
Wata ran mutum kai dada munana mai
Wata ran mutum ai yakan dadada ma
Wata ran mutum kai kake dadada mai
Oh dan adam mai wuyan gane hali
Oh-oh bil adam mai wuyan gane hali
Sha'anin mutum ni yakan firgita ni
Lamarin mutum ni yakan jijiga ni
Lamarin mutum ni yakan maguza ni
Sha'anin mutum to ikan bani haushi
Wata ran mutum to ikan dadada min
Haba bil adam mai wuyan gane hali
In anyi ruwa kace anyi ruwa
In anyi sanyi kuce anyi sanyi
In anyi rana kuce anyi rana
In anyi zafi kuce anyi zafi
Oh dan adam mai wuyan gane hali
In anyi rana kuce anyi rana
In anyi ruwa kuce anyi ruwa
In anyi sanyi kuce anyi sanyi
Sha'anin mutum ni yakan bani oh-oh
Gashi chan mutum mai wuyan gane hali
Oh dan adam mai wuyan gane hali
Oh dan adam mai wuyan gane hali
In kayi keke ice kayi keke
In kayi babur ice kayi babur
In kayi moto ice kayi moto
In kayi gida ice kayi gida
In kaki gida ice kaki gida
Mutum baida gadon ka wallahi Allah
Amma ina dai da gadon batunka
Oh bil adam mai wuyan gane hali
Gashi bil adam mai wuyan gane hali
In kayi riga da hula kagane
Dan adam zai ce ai ko kayi
In kayi wando ice kayi wando
In kayi hula ice kayi hula
In kayi riga ice kayi riga
In kayi aure ice kayi aure
In kaki aure ice kaki aure
Mutum baida gadon ka wallahi Allah
Amma ina dai da gadon batunka
Allan da yayai dan adam dai ka gane
Shine kawai jallah ne ke iyar mai
Oh dan adam mai wuyan gane hali
Haba bil adam mai wuyan gane hali
Wani yayi riga da wando ko mai kyau
Yayi hula kagane ko mai kyau
Sanan ku gane ya hau wanga moto
Tuki yake duk inda ka ganshi
Sai kace wane mai arziki ne
Yaya kasan nan cikin zuciyar sa
Ko bil adam mai wuyan gane hali
Takan tara wanga ai baida awu
Babu riga ta kirki jiki nai
Kace wane ai ina dai talauci
Yaya kayi har kasan zuciyar sa
Sha'anin mutum mai wuyan gane hali
Oh dan adam mai wuyan gane hali
Wata ran mutum ai yake kyautata ma
Wata ran mutum kai kake kyautata mai
Wata ran mutum kai kake munana mai
Wata ran mutum shi yake munana ma
Gashi chan mutum mai wuyan gane hali
Oh dan adam mai wuyan gane hali
Babban gida harda gadi ka gane
Su dan adam mai wuyan gane hali
In anyi rana ice anyi rana
In anyi sanyi ice anyi sanyi
In anyi ruwa ice anyi ruwa
Allan da yayai dan adam dai ka gane
Shine kawai jallah ne ke iyar mai
Haba bil adam mai wuyan gane hali
Haba bil adam mai wuyan gane hali
Wata ran mutum shi yake munana ma
Wata ran mutum kai kake munana mai
Wata ran mutum shi yake taimaka ma
Wata ran mutum kai kake taimaka mai
Wata ran mutum shi yake taimaka ma
Wata ran mutum kai kake taimaka mai
Wata ran mutum shi yake agaza ma
Wata ran mutum kai kake agaza mai
Allan da yayai dan adam dai kagane
Shine kawai jallah ne ke iyan mai
Sannu bil adam mai wuyan gane hali
Dan adam mai wuyan gane hali
In kayi wanan ice kayi dai-dai
In kaki wanan ice kayi dai-dai
Sha'anin mutum ni ikan firgita ni
Sha'anin mutum ni ikan firgita ni
In kayi keke ice kayi keke
In kayi moto ice kayi moto
In kayi moto ice kayi moto
Mutum baida gadon ka wallahi Allah
Amma ina dai da gadon batunka
Sha'anin mutum mai wuyan gane hali
Haba bil adam mai wuyan gane hali
Mutum baida gadon ka wallahi Allah
Amma ina dai da gadon batunka
Kai dan adam mai wuyan gane hali
Oh dan adam mai wuyan gane hali
Wata ran mutum ni yakan firgita ni
Sha'anin mutum ni yakan jijiga ni
Sha'anin mutum ni yakan firgita ni
Wata ran mutum ai yakan munana mun
Wata ran ko mutum yakan kyautata mun
Oh dan adam mai wuyan gane hali
Gashi chan mutum mai wuyan gane hali
Written by: Adamu Dan Maraya Jos