album cover
Shugaba Adali (Version 1)
50
World
Shugaba Adali (Version 1) was released on April 24, 2018 by Apple Media Africa as a part of the album Iconic Sounds of Africa, Vol. 97
album cover
Release DateApril 24, 2018
LabelApple Media Africa
Melodicness
Acousticness
Valence
Danceability
Energy
BPM142

Music Video

Music Video

Credits

PERFORMING ARTISTS
Mudassir Kasim
Mudassir Kasim
Performer
COMPOSITION & LYRICS
Mudassir Kasim
Mudassir Kasim
Composer, Lyrics

Lyrics

Na fada maki sirrikan Raina gaskiyar zance ina sanki
To kiyarda dani
Na fada maka sirrikan Raina gaskiyar zance ina sanka
To kayarda dani
Na fada maki sirrikan Raina gaskiyar zance ina sanki
To kiyarda dani
So guda daya ba'a kasaptashi dan mutane biyu su amfana
Bashida lakani
Eh ra'ayi na ni soyayya, zuciyata yau kin sace
Acikin 'kauna na dace, wasu nacewa na zauce
Ita soyayya kurmace, notin kaina ya kwance
'kauna ta rinjayeni na 'dimauta saboda in sanki
So guda daya ba'a kasaptashi dan mutane biyu su amfana
Bashida lakani
Eh ko akai zakaiman shaida, raina ansan ina sanka
Tinda mun zauna mun saba, a cikin rai bana shakka
Yi tunani gunka sai inji kamar ma ba tamkar ka
Gudun 'bacin ranka nike koda wasa bana tsaki
So guda daya ba'a kasaptashi dan mutane biyu su amfana
Bashida lakani
'Karshen so dai aure ne kar kinyada miji naki
Maganar ji ko zaki babu kamar abban 'ya 'yan ki
Wanda in ranki zai gita, dake zaunawa 'daki
In toshe masa garbu sila taso ba 'kwaron baki
So guda daya ba'a kasaptashi dan mutane biyu su amfana
Bashida lakani
So guda daya ba'a kasaptashi dan mutane biyu su amfana
Bashida lakani
Ba arai in za'ayi baya abokin da ake sirri
Tattali harda rukon da nake maka tamkar 'dan jariri
A aminta da nagarta kai naiwa kallo na bugu 'kari
Miji na ne kai zanaiwa batun danko a idon baki
So guda daya ba'a kasaptashi dan mutane biyu su amfana
Bashida lakani
Eh a wani kogi nai nitsewa
Gareni ba hanyar fitowa
Ziran mayafi nai rikewa
Jikina tsini kin cakawa
Bani kaiwa in na cire sanki
So guda daya ba'a kasaptashi dan mutane biyu su amfana
Bashida lakani
Ni nakai a masoyinki, in an 'daura mizanai
Sama in zaki haurawa, ki kusanto nan ga tsani
Duniyar nan an shela sanki bamai iya kamo ni
Da Sarewa zanyo busa na hada maki harda ta kakaki
So guda daya ba'a kasaptashi dan mutane biyu su amfana
Bashida lakani
Eh na fada maki sirrikan Raina gaskiyar zance ina sanki
To kiyarda dani
Ah na fada maka sirrikan Raina gaskiyar zance ina sanka
To kayarda dani
Na fada maki sirrikan Raina gaskiyar zance ina sanki
To kiyarda dani
So guda daya ba'a kasaptashi dan mutane biyu su amfana
Bashida lakani
Written by: Mudassir Kasim
instagramSharePathic_arrow_out􀆄 copy􀐅􀋲

Loading...