album cover
Kiyardadani
329
World
Kiyardadani was released on July 6, 2018 by Apple Media Africa as a part of the album Tribal Grooves, Vol. 30
album cover
Release DateJuly 6, 2018
LabelApple Media Africa
Melodicness
Acousticness
Valence
Danceability
Energy
BPM139

Music Video

Music Video

Credits

PERFORMING ARTISTS
Umar M Sharif
Umar M Sharif
Performer
COMPOSITION & LYRICS
Umar M Sharif
Umar M Sharif
Composer, Lyrics

Lyrics

La la ki yarda da ni zancen da nake miki
Soyayya ba zai kyau da mu ba
Cikin raina akwai wacce na aje
In cire ta ba zan iya ba
Eh ka yarda da ni zancen da nake maka
Soyayya mun dace ka duba
Maganar iyaye ka zam mai biyayya
Ya kamata mu daidaita juna
Eh ni na yarje da kai za na zauna
Matsayin mijin aure na
Ka zamo jagora a guna
In kira ka uban 'ya'yana
Zan ma biyayyar aure da amana
Zan kare hakkinka mijina
Ka yarda da ni ka ce in zo mu zauna
Zuciya ta za ta ji dadi
Ki yarda da ni zancen da nake miki
Soyayya ba zai kyau da mu ba
Maganar iyaye ka zam mai biyayya
Ya kamata mu daidaita juna
Dukkan rai yana da abin so
Yai zama da shi yake da muradi
Ke ko kin amince a kan so
Ni kike ta yi wa zumudi
Ni ko a raina da wadda nake so
Mu yo zama da ita mai dadi
Hakuri da kaina na ba ki
Soyayya ba zan yo da ke ba
Eh ka yarda da ni zancen da nake maka
Soyayya mun dace ka duba
Cikin raina akwai wacce na aje
In cire ta ba zan iya ba
Ka dube ni daga sama har kasa
A jikina mene ne na rasa
Za ni so a ce ka matso kusa
Ka taimaki rai kar da ka yo kisa
A ido kar ka zubo kasa
Hanya ta wucewa in rasa
Maganar iyaye ce ta sa
Na taho mu daidaita juna
Ki yarda da ni zancen da nake miki
Soyayya ba zai kyau da mu ba
Maganar iyaye ka zam mai biyayya
Ya kamata mu daidaita juna
Kar ki ce mini haka zo ki jiya
Ke 'yar uwata ce bisa gaskiya
Ke ma akwai wani na nan a duniya
Ke kaɗai ya sanya a zuciya
Da zai furta miki za ki ce na kiya
Don ba shi kika sanya a zuciya
Da ni da ke sam babu kiyayya
Ki bar batun so inai miki magiya
Eh ka yarda da ni zancen da nake maka
Soyayya mun dace ka duba
Cikin raina akwai wacce na aje
In cire ta ba zan iya ba
Eh ka yarda da ni zancen da nake maka
Soyayya mun dace ka duba
Maganar iyaye ka zam mai biyayya
Ya kamata mu daidaita juna
Written by: Umar M Sharif
instagramSharePathic_arrow_out􀆄 copy􀐅􀋲

Loading...