album cover

Daraja

41,275Blues2023
album cover
00:00
00:10
00:15
00:25
01:40
02:20
02:45
03:00
03:15
05:45
00:00
06:05
Past 7 Days
Daraja was discovered most frequently at around 3 minutes into the song during the past week

Lyrics

DARAJA
Bakin ganguna matsattsaku zauna can tafiya ba ra'ai ba a yi ta da ni ba,
Bin gayyar Na'ayya taka kayar dundu ba kuma zan bi tarkacen yuyu ba,
Na san ban zama abin so gun kowa kuma kowa ba zai zamo min makiyi ba,
Bar mai dariya ya wassafa tunbele ran kukansa ni ba zan ki na kalla ba.
***
Farfesa ba za ni raina mafari ba,
Farfesa ba za ni tsufa a zance ba,
Farfesa ba za ni kori masoyi ba,
Farfesa ba za ni gwasale manya ba,
Farfesa ba za ni manta mugunta ba,
Kuma kun san ba na ki yafe mugunta ba,
Allah Khalikinmu Shi ke raba baiwa,
Farfesa ba zan kukumta ilimmi ba,
Jahilci ba zai zamanto riga ba,
Tafiyar hankali take saka tsinkaya,
Wani baitin da nai ku bar saka rudani,
Mai neman kahon kare ne wahalalle,
Ko da an raka shi ba zai samo ba,
ba zai samo ba,
Ko da an raka shi ba zai samo ba.
***
Sirrin darraja ku ce ajiyar Allah taskar baye-baye na nan a jarabta, Farfesa a kan kadarko na jarabta fatana na tsallake ba wayo ba.
1
Tsantsar darraja mu je gun manzona Annabi dan Amina gata gun kowa,
Dukkan baye-baye na nan a kadarko wani shinge da ba a yi masa gaugawa,
In ban gode Zuljalalu ba me zan yi Wanda ya jarraba ni babu idon kowa,
Wasu sun ce da ni ina wahalar banza ga ba su tattaro sanin Allahna ba.
2
Kun ga a duniya mutum hudu zan gaisar farko zana fara gaida mahaifana,
Sannan gaisuwa gare ku masoyana daga nan gaisuwa wa tarin makiyana,
Kun san duniyar ga ba don makiya ba Farfesan waka gida za ni na zauna,
Mafaraucin kurakurai ke maka kaimi sai ka yi gyare-gyare tun ba a kalla ba.
3
Bakin ganguna matsattsaku zauna can tafiya ba ra'ai ba a yi ta da ni ba,
Bin gayyar Na'ayya taka kayar dundu ba kuma zan bi tarkacen yuyu ba,
Na san ban zama abin so gun kowa kuma kowa ba zai zamo min makiyi ba,
Bar mai dariya ya wassafa tunbele ran kukansa ni ba zan ki na kalla ba.
4
Na ga wadansu masu yi don Rabbani na ga wadansu masu haddasa rudani,
Fadin illimi yake sa sabani amma mabiya suke cin amfani,
Da na zo duniya na gane ana karya daga nan bil'Adam ya fantsama bin hauni,
Ga almajirinku Farfesan waka mai wakar da bai wuce dan koyo ba.
5
Ni ba so nake in fi ku iyawa ba ban cewa waninku na iya wake ba,
Amma me ake fadi harshen Hausa in ba a san mutum akan aiki nai ba,
In kun ba ni faskaren bishiyar marke kwana shabiyar ba zan wuce wannan ba,
Ku sani 'yan uwa ba zan yi da wasa ba kudar gatarin mako biyu zan diba.
6
Waka abinda babu gun mara azanci babu kan jahili ko babu akan wawa,
Wata baiwa da ke a harshen mai zance hikima mai tasarrafin tafiyar giwa,
Su kwakwalwa da hankali na tantance harshe makogwaro da lebba da fitarwa,
A takaicen da bai azabtar saurare waka mai abinda wayo bai yo ba.
7
Ga cikason mutum na huddu masoyana wanda fara gaisuwa a kashin farko,
Malamaina da tarbiyarku nake komai hasken illimi yake sa kai karko,
Su ne ke dafa ka ba da tukunya ba ka shigo duniya ashe sun zam jigo,
Tammat! Hamdala ta tabbata gun Sarki mu bayin da wanzuwa ba ta aura ba.
***
Sirrin darraja ku ce ajiyar Allah taskar baye-baye na nan a jarabta, Farfesa a kan kadarko na jarabta fatana na tsallake ba wayo ba.
To lallai muna kadarko na jarabta fata za mu tsallake ba wayo baaaaaa...
~SULAIMAN FARFESAN WAKA~
Written by: Farfesan Waka

Shazam Footer

Select language:
Google Play Store
Apple App Store
Chrome Web Store
Galaxy Store

Follow Us

Loading...