Lyrics
[Verse 1]
Eh! Gimbiyar mata, zan wa wakena
Amira mai kyawun halayya 'yar gidan girma
[Verse 2]
Gimbiyar mata, Amira son kowa
Sannunki mai kyawun halayya 'yar gidan girma
[Verse 3]
Gimbiyar mata, Amira son kowa
Sannunki mai kyawun halayya 'yar gidan girma
[Verse 4]
Eh! Ki ji ni wakene zan fara da sallama farko
Gareki mai takun kasaita da jiniyar baiko
Ko da cikin 'yan mata duban da nai kina farko
Mai kyan hali ga ki da tarbiyya kina da alfarma
[Verse 5]
Gimbiyar mata, Amira son kowa
Sannunki mai kyawun halayya 'yar gidan girma
[Verse 6]
Eh! Amira kyakkyawar 'ya ki ji ga ki mai dirin tsaiwa
Tattabara sarkin alkawari ke nai kira giwa
Yawan hakurinki ya sa ni zan kira ki son kowa
In na yab amiki ana ce min me ye nake nema
[Verse 7]
Gimbiyar mata, Amira son kowa
Sannunki mai kyawun halayya 'yar gidan girma
[Verse 8]
Eh! Farin jini ne ya sa sunanki ke ta shawagi
Balbela ce ke ba mujiya ba da ba ta yin wargi
Sa'arki na mota ke tauraruwa kina jirgi
Da ke kwaye in kun jera jikinsu na kyarma
[Verse 9]
Gimbiyar mata, Amira son kowa
Sannunki mai kyawun halayya 'yar gidan girma
[Verse 10]
Gimbiyar mata, Amira son kowa
Sannunki mai kyawun halayya 'yar gidan girma
[Verse 11]
Eh! Mai son ki shi ma dan baiwa ne idan ya same ki
Kularki in dai ta biyo kansa zai yi mamaki
Tsafta da kyau har da yawan gashi an akwatancenki
Dauko madubi ki ga kayinki Amira mai kima
[Verse 12]
Gimbiyar mata, Amira son kowa
Sannunki mai kyawun halayya 'yar gidan girma
[Verse 13]
Eh! Komai nace ni a kan ki Amira ba zuga nai ba
Idon mutane shi ne sahida ba zan yi karya ba
Haske na rana tafin hannu ba zai tarewa ba
Ke inuwa ce ko ko laima gari ake nema
[Verse 14]
Gimbiyar mata, Amira son kowa
Sannunki mai kyawun halayya 'yar gidan girma
[Verse 15]
Eh! Amira in dai zata yi magana ta kan yi mai taushi
Ga tafiya tata cikin nutsuwa jikinta na kamshi
Kun ji ni ina ta fadin kyawo idonta ne mashi
Kowa ta harba da tai saiti dole tai sama
[Verse 16]
Gimbiyar mata, Amira son kowa
Sannunki mai kyawun halayya 'yar gidan girma
[Verse 17]
Eh! Gimbiyar mata, zan wa wakena
Amira mai kyawun halayya 'yar gidan girma
[Verse 18]
Gimbiyar mata, Amira son kowa
Sannunki mai kyawun halayya 'yar gidan girma
[Verse 19]
Gimbiyar mata, Amira son kowa
Sannunki mai kyawun halayya 'yar gidan girma
Written by: Isa Gombe, Isa Gombe, Mubarak Dutse & Farouk M Inuwa, Mubarak Dutse, RR