album cover
Saudat 2
9,501
Afro-Pop
Saudat 2 was released on April 27, 2018 by Abnur Entertainment as a part of the album Matan Gida
album cover
Release DateApril 27, 2018
LabelAbnur Entertainment
LanguageEnglish
Melodicness
Acousticness
Valence
Danceability
Energy
BPM

Music Video

Music Video

Credits

PERFORMING ARTISTS
Nura M. Inuwa
Nura M. Inuwa
Performer
COMPOSITION & LYRICS
Nura M. Inuwa
Nura M. Inuwa
Composer, Lyrics
PRODUCTION & ENGINEERING
Nura M. Inuwa
Nura M. Inuwa
Producer

Lyrics

Burin duniya na ganni a tare da kai
Saudatu ce burin zuciya, tashiga 'bargo har jijiya
Al-'kawari dama na rika mai sona bazan barta ba
Kai ka zamo burin zuciya, kashiga 'bargo har jijiya
Dadi koma acikin wuya, mai sona bazan barka ba
So sanadi mai sa zuciya, tayi gamo bada shirinta ba
Inta fada in aka 'kiyi mata, ai tsintar kai acikin wuya
Eh so ya sarke man zuciya, yabi jikina ya kewaya
Saudatu in ban ganta ba, zan cigiya ko in tambaya
Tinda na dakko al-'kawari, ko nai nisa zan waiwaya
Saudatu kin zam raba gardama, wacce takai ke banganta ba
So sanadi mai sa zuciya, tayi gamo bada shirinta ba
Inta fada in aka 'kiyi mata, ai tsintar kai acikin wuya
Tinda nasame ta nasan, nai gamnakatar haka na anbata
Ko 'kishi sirrin ruhi ba'a sani sai inya fita
Raina kama sai kaga kayi hakan so kayi mani bazata
Yarda kadauken haka nan nake, share hawaye na zai zuba
So sanadi mai sa zuciya, tayi gamo bada shirinta ba
Inta fada in aka 'kiyi mata, ai tsintar kai acikin wuya
Eh 'kauna har tai sansani sai tafi karfin gangar jiki
Dukkan rayuwa na barmaki ke kika zamto mai mallaki
Aiki inzakiyi karki jira ki kirawoni mu taimaki
Zan iya yin komai kirike wannan karki fargaba
So sanadi mai sa zuciya, tayi gamo bada shirinta ba
Inta fada in aka 'kiyi mata, ai tsintar kai acikin wuya
So sanadi mai sa zuciya, tayi gamo bada shirinta ba
Inta fada in aka 'kiyi mata, ai tsintar kai acikin wuya
Eh kan so bashi baka bini ba kai nai nuni acikin 'dari
Da mun faro daga badini yayi yawa gashi a zahiri
Domin neman dankon so waye yasa kaman kyautar yari
Na karba nai alfahari, duk tsanani bazan barka ba
So sanadi mai sa zuciya, tayi gamo bada shirinta ba
Inta fada in aka 'kiyi mata, ai tsintar kai acikin wuya
Eh riba ta zama tare dake na yaba kyau naki da hankali
Mai hakuri tareda tarbiyya mai samar da tawakkali
Zanyi kula gun tare hakkin ki a gida zan zama adali
Ga sarki nabi na sarauniya, ja ragamata tawu muje gaba
So sanadi mai sa zuciya, tayi gamo bada shirinta ba
Inta fada in aka 'kiyi mata, ai tsintar kai acikin wuya
Eh nayo sa'ar babban rabo wanda dashi ban iya sa-in-sa
Sonsa ya kaudar da sukuni walla 'kiris ma in karasa
Nayi aminci na gazgata so komai yana iya haddasa
Banda kamar kai nan duniya indai har babu Uwa Uba
So sanadi mai sa zuciya, tayi gamo bada shirinta ba
Inta fada in aka 'kiyi mata, ai tsintar kai acikin wuya
Saudatu ce burin zuciya, tashiga 'bargo har jijiya
Al-'kawari dama na rika mai sona bazan barta ba
Kai kazamo burin zuciya, kashiga 'bargo har jijiya
Dadi koma acikin wuya, mai sona bazan barka ba
Written by: Nura M. Inuwa
instagramSharePathic_arrow_out􀆄 copy􀐅􀋲

Loading...