Adbull D'in En Sevilen Şarkıları
Şarkı sözleri
Eh yeh kin bakanta mani
Ta faranta mani
Ga tsiya kin mani
Ita ko arziki taimani
Arayuwar da mukai nidai ina ganin na 'bata
Itace tai cigiya danazo godiya nai mata
Kin sani yin kuka, innai zance ki tanka
Duk sanda na farka na tunoki sai inji ya haka
Ita kyakkyawa ce
Ana fadin na dace
Abokanai sun tantance
Asanta wai na nace
Ga waya na rike kirata ko ina ma take
Mu rayuwa babu ke
Kuma nasan hakanan kike
Son ki ni na soma
Cikinsa babu nadama
Zuciya kika kama
Eh ke kinsani na suma
Sanadin halinki ne shima
Lokacin ina tayin rama
Wasu ko suna tayin gulma
Ina rasa gane kanki
Kamar da iskokai kanki
Ana fadin in 'kyaleki
Ruwan ido ya cika gunki
Duk da haka na soki
Inata rokon sauki
Gaskiya kika 'boye
Akwai wanda kika sauye
Hakki naso kin tauye
Kin taba fada mini
Da wasa kikai mani
Shine kike yawan dai gani
Zuciyarki ya shiga har jini
Dukda ya yaudare ki
Nikuwa na tallafe ki
Gashi kin sani raki
Kinki sauyo halinki
Kina nan akan bakarki
Maimakon ma 'kawarki
Shawara ma ta baki
Aurenki zaifi
Dakintayin laifi
Inganki kedashi zafi
Dama wanine zaifi
Ina tayin dogon hange
Acen nasamo wata Bilki
Tasani bana yin waige
Ki hakuri in na mangareki
Meyasa ma nasanki
Babu hali in soki
Akan kine wasu mutane
Da zan wuce na kasa kunne
Sunkace ni mayaudari ne
A kofar gidan su A'i
Bayan sallar Isha'i
A shagon kawun su A'i
Dan a hanani A'i
To munyi sallah du'a'i
Ciki ma munyo du'a'i
Allah ya kauda 'yan bala'i
Muyi aure da A'i
Mu samu zuri'a da A'i
Ke kuma na yafe maki
Tsakanin mu babu hakki
Allah ya nunan aurenki
In figo kudi abaki
Inba makiya mamaki
Nine dan uwanki
Kema zaki zoki
Bikina da mijinki
Yiriri zanyi murnaah
Lyrics powered by www.musixmatch.com