歌词
[Verse 1]
Eh! Kauna nake bara ba ni dalili na tunzura
Ga shi kin ki ki yi na'am zuciya ta ki hakura
[Verse 2]
Eh! Na zata turmi kadai ke jurara yawan daka
Sai ga zuciya na duka kamar ana haka
Duk abin kasa na kaji ne za su tsattsaka
Ciwon zuciya shin me ke ba shi waraka
[Verse 3]
So rabbi ke sakawa mutum ki tuno haka
A jikin gyada ake samun mai da mutsttsika
Dutse ya yi ido inda ruwa ya bubbuka
Kauna ba ta fita ciwo ne da ke jika
[Verse 4]
Shekaru shida muna soyayya misalika
Kuma mun yi alkawar wand ana kasa tsallaka
Tunda fari maganar aure an yi da baka
Har manyanmu suka yi shaida zan yi mallaka
[Verse 5]
Sharadin da ya biyo baya na aza shi ka
Na bidar ci gaba don iliminki ya habaka
Zan iya abin da zan in kin zo da bukatuka
Ban zaton za ki gujen in kika samu daukaka
[Verse 6]
Tafiya muna ta yi sannu a sannu mu duka
Shekaru suna ta ja lokaci na ta raraka
Duk sa'anni nawa sun yi gidaje da filika
Sun aure sun aje matayensu cikin daka
[Verse 7]
Ni ina shago da 'yan kayana a daka
Ke dai nake jira kana na samu wattsaka
Diploma kin gama yadda na fara tsaruka
Daga nan za ki tsaya mu yi aure mu lulaka
[Verse 8]
Akasi nake gudu kika ce za ki dan raka
Digiri za ki yi nai uzuri zai fi saukaka
Sai na takura wa rai tunda na taka tsaunuka
Na fada na hakura zan aje 'yan sulalluka
[Verse 9]
Kun ga tashi sannu ne gamji na jure sassaka
Bege ina ta yi gun ki har ma da baituka
Wasu ma suna kiran zuciya ta ta karnuka
Ba komai kan ki nai nazari so ne ya saka
[Verse 10]
'Yan uwa sun gaji ta kai da sun fara caccaka
Ni ban matsa miki ka da rai yai ta fincika
Komai da lokaci gama surfe da sussuka
Wa'adin gama karatunki ya zo da baraka
[Verse 11]
Nisan da kin ka yo a makaranta ya farrakka
Kin dau dukkan zuga da ake miki ko nika
Shi hukuncin da kika yi ya sa rai na babbaka
Kin yada alkawar kin bar raina da cutuka
[Verse 12]
Ki tuno wahalhalun da na yo kanki ki yi nika
Lokaci guda ki ce ba ki son na ban da mafaka
Hakuri dole zan yi kaddar na ji zan rika
Amma hakkina na kanki ba ya bar ki ba
Written by: Nura M. Inuwa


