音乐视频

音乐视频

制作

出演艺人
Hamisu Breaker
Hamisu Breaker
表演者
作曲和作词
Hamisu Breaker
Hamisu Breaker
作曲

歌词

Dawo Hamra ʼyan mata
Labarin ƙauna kawai daɗi wani saʼin so akwai ɗaci
Na zautu a kan ki ba bacci, so ya sanya ni lalaci
Zuma ta zam mini maɗaci Hamra ki juyo sai na ji daɗi
Labarin Hamra zan ba ku, Hamra ʼyan mata
Wata ranar Sallah ne hawan Ado Bayero na ƙarshe
In za ku tuna hawan Ɗorayi hawan Ado yana yi
Na fito ni da abokai na mu mu biyar a kyawun yanayi
Kallon komawar sarki, waigen da na ɗan yi
Na ga wani wal-wal haka hasken idanun Hamra ya janye raʼayina
Su su uku ne, amma tunanina Hamrat ta zo gu na
Zuciya ta na raya min in je kusa in yi bayanin kai na
Sai na ɗan juyo na cewa abokin a B Malik nai kamu
Ya ce mini me ka samo
Abdul Respect ya ɗan yi murmushi ya dake ni ya ce abokina
Wata yarinya a gefenka na ga kamar ƙalbinta kwai ƙauna
B Malik sai yace mu ɗan ƙarasa mu yi mu su jawabi mana
Maʼanarsa jawabin ƙauna
Sai na ɗan karasa na yo sallama a gareta ta amsa mini
Sai nace baiwar Allah akwai gu nan ko a ɗan gusa mini
Sai ta yo wani murmushi wanda duk yanayina ya daɗa mini
Sai tace min malam ɗan dakata haka kar ka takura mini
Amma ba komai dob na sani soyayya ce ta ja mini
Sai na ce mata kin ga sunanki ne fa kawai za ki ɗan gaya mini
Umar Nas Don ya ɗan ƙaraso sai yace mata kin ga ʼyan mata
Shi ya ƙarasa duk jawaban da zan shi ya furta mata manufa ta
Mun yo nasara don mun yi sabo sosai ni da shi da ita
Har Sarki ya wuce mun wuce dukaninmu muna ta bankwana
Sai wata rana
Mun dawo hanya Ɗan shaba sai ya taɓo ni yace abokina
Yaya sunan budurwar da kai ne ko kuwa aʼa ba suna
Sai na ɗan yi shiru ina yin tunanin shin wai ta gayan suna ko ba ta faɗa min ba
B Malik sai ya ce mu koma in rai da rabo wata ƙila ma dace
Ai ko mun dace
Na tambayi sunanta sai ta ce min wai sunanta ita ɗata
Sai ta nuna min ƙawarta ta ce mini wanna kuma wai goba
Ɗayar da ta ƙaraso ta ce da ni ni kuma sunana yalo
To kai yaya sunanka
Sai na ce sunana Hamisu Breaker Dorayi haka suna na
Sai Hamra ta ƙaraso tace da ni sunana na gaskiya Hamra
Eh kwarai Hamra
Sai na ce a ina take ta ce da ni Nasarawa a nan ne ta zauna
Ƙawarta ta ce da ni aʼa mu a Kaduna muka yi yo zauna
Ba ʼyan Kano ne ba
Suka ban lambar waya wadda za na kira su mu dinga gaisawa
Mun fara waya da su haka mai daɗi sun ɗeben kewa
Daga baya idan na kira su sai in ji layin ya yi yankewa
Layin an kullewa
Wayyo Allah na Hamra (Dawo Hamra ʼyan mata)
Na dena ganinki Hamra (Dawo Hamrah ʼyan mata)
Jin muryarki Hamra (Dawo Hamra ʼyan mata)
Yaya zan yi na gan ki Hamra
Written by: Hamisu Breaker
instagramSharePathic_arrow_out

Loading...