歌词
A bar mu nida ke
Indai soyayya ce
Sareena na fada
Kece cikon buri na
Sareena taka ce
Indai da alkawari
Raba mu zai wuya
Tsantsar soyayya ce
Na dade idanuwa nason su gano naki
Zuciya ta koda yaushe tana mararin kallonki
Allah mai iko koda yaushe ba mamaki
Sai dai muji kamshin juna idanu basa aiki
Zanyi kokari farincikin ki ya daure
Kema kin sani nafi son a ganmu a tare
Karda ka damu akwai mai kallo
Allah baya bacci
Shi zai tsare mu ya bamu abinci
Kuma ya tsare mu da kunci
Shi ya bamu soyayya mai zaki
Bata hado da madaci
Koda yaushe baka yi mini nisa
Bare muyi zama na kadaici
In naji sautin muryar da ba taka ba (Sareena)
Sai na rude ko zuciya ta ta kulle
In banji ka ba
Ahh ahh
Nagode da wannan kalame
Ki sanya naji ni da tarin mukame
Sareena ta, ta wuce tsarin kazame
Nayi godiya da wanga kalami mahimme
Da sanki nake rada zan ma banba
Soyayya baza ta zamo kuskure ba
Zuciya ta zama tamkar idanu
Kai nake bi dan Allah jani sannu
Kar kayi mamaki idanun ka sunyo kananu
Kar kayi mamaki ina ganin ka, kabi sannu
Nasan kina ji na
Bakya gani na
Kullum kike ji na
Written by: abdulkadir tajuddeen


