制作

作曲和作词
hamisu said yusuf
hamisu said yusuf
词曲作者

歌词

[Verse 1]
Kida
Lokacin da ina dako
Rayuwa ta dan rako
Wahala tai min jiko
Farin ciki ban san shi ba
[Verse 2]
Hana rantsuwa na tino
Rana guda na ji dandano
Ran da nai baban gamo
Labarin nake so in gino
[Verse 3]
Ranar ina bakin aiki
Sai na ga wata ta yo birki
Abin da ya ban mamaki
Sai tace malam taso
[Verse 4]
Aiki nake so in biya
A yanayin ta da tarbiyya
Ina zatonta da kyan aniya
Dama fa na ci bakar wuya
Ban samu abinci ba ko daya
[Verse 5]
Ku bini a sannu a sannu don jin ta ya ta kasance
Na dauki kayan amma ban kai ba sai da maraice
Don gidansu da nisa na sha wuya a takaice
Sai ta gaya mini cewa dan dakata karka zarce
[Verse 6]
Sai da na kai kayan, tai tambayar sunana
Ko da taurin kaina sai nace ki bani kudina
Kana tace number na zan bata don wata rana
[Verse 7]
Kash! nace ina gabas kina yamma
Don Allah sallame ni da himma
Kin ga na gaji sosai ga jikina ya dau kyarma
Tace da ni in yin hakuri in ci abinci kan in koma
[Verse 8]
Sai nace na gode ina zaune nai ta tunani
Shin wannan wace ce za ta zo haka nan ta tare ni
Bayan na kammala cin abinci tayi mini kyauta mai girma
Ta ba ni har numbarta don kirata in na koma (Na koma)
[Verse 9]
Ai ko ina komawa sai na kirata don mata godiya
Sai ta amsa wayata na fara zance tanai mini dariya
Ai ko nai ta yabata don zatona shi ne godiya
[Verse 10]
A hankali mun yi sabo amma akwai wata matsala babba
Gidansu ba sa so na da cin mutunci ba zan jure ba
To ku biyo ni a sannu ba anan kizo yayai sakar ba
Don na fara tunanin rubuta waka in rerawa
[Verse 11]
Lokaci banza yabar ni na bayyana labarin nan duka ba
Sai ku biyo ni a sannu
Sai da kai
Midget Mix
Kida
Written by: Hamisu Breaker, hamisu said yusuf
instagramSharePathic_arrow_out

Loading...