制作
出演艺人
Nazir M. Ahmad
表演者
作曲和作词
Nazir M. Ahmad
词曲作者
歌词
[Intro]
Uhm, uhm, uhm ya
Uhm, uhm, uhm
Uhm, uhm, uhm, ya
[Verse 1]
Ina ma da arziƙi masoyi ya san dai ya na da gata nai
Ina ma da ilimi in nusar da mai so halin ma'aiki nai
Ina ma da tausayi masoyi in yafe shi dukka laifi nai
Ina ma ina ga sai Arewa ba sa kushe ta su baiwa ba
Ina ma da maganin na bai wa masoyi ya kore cuta tai
Ina ma da dukiya na badda wa mai san rufin asiri na
A ce zan faɗa a ji masoyi ba zai tauye masu nema ba
A ce za ni aikata a ko ya, ba a kushe masu gyara ba
Idan zan faɗa a ji, masoyi ba zai zagi shugabanni ba
Ina ma da ɗan tsaki masoyi da yunwa ba sa ga juna ba
[Verse 2]
Wasu mafaɗa oyoyo baba Buhari kuɗi suka nema
Wasu mafaɗa oyoyo na yi dan daɗa suna suma
Wasu mafaɗa oyoyo ba don kishi sunka faɗa ba
[Verse 3]
Buhari ya zama abin tallata hajjar waƙar kowa
Buhari ya zama abin kushe, an ce "ya hana kowa"
Waɗansu suna ta faɗin dama ya mutu, ya zama gawa
Buhari ake zargi ya hana yin safarar shinkafa
[Verse 4]
Kai mu ɗauka e haka ne, to mene laifin sa Buhari?
To mu tambayi kakanni ƙasarmu a da an san ta da noma
Ƙasashe sun fi biyyar wanda mukai wa silla suka girma
Ashe gyaran kayan ka bai zama sauke mu raba duk ba
[Verse 5]
Waɗansu mu basu iri su koma can a ƙasar su, su noma
Da shi suka ci suka sha kuma su yi wa ƙasa ta su hidima
Ni abin da nake tsoro ba saukar sa a mulki ne ba
Ni abin da nake tsoro ba wanda zai maye gurbi ne ba
Mun shiga ƙunci bara ana ta kashe mu muna daɗa ɓuya
A bi mu wurin bauta, a bi mu gida a kashe mu da 'ya'ya
[Verse 6]
Mu muna ta dua'in Allah canja yanzu da canjin yaz zo
Muke ta ɓarin zance, mu zama kamar kambu suka murzo
In munka butulcewa Allah kamar amba mun furzo
Shin mun gode kenan? ko kuma mun kyauta kenan?
In Allah ya yi fushi, mu san da sani mune muka jawo
Wa ke da sanin gaibu? ko zance na akwai aibu?
[Verse 7]
Wasika zuwa ga shugaban ƙasa, wasika zuwa ga shugaban ƙasa
Mai tsaro bai tsoro a tsakar tsanani koda an ce ya bar ƙasa
Wasika zuwa ga shugaban ƙasa
Ka ga tudun da ka hau da kyar mai sauke ka sai dai wanda yai ƙasa
Wasika zuwa ga shugaban ƙasa
Wanda ya yi ka mutum mai jama'a ne ya nufa ka yi shugaban ƙasa
Wasika zuwa ga shugaban ƙasa
Ba shirka ka yi ba a hawan ka dalillin nan bai sa ka sha ƙasa
Wasika zuwa ga shugaban ƙasa
[Verse 8]
Waɗansu suna tsafi, waɗansu suna addu'a Allah sa ka sha ƙasa
Wasika zuwa ga shugaban ƙasa
Ka sake riƙe Allah, Baba akwai nisa hanya ta gaskiya
Wasika zuwa ga shugaban ƙasa
Ka sake riƙe Allah Baba da ɗaci duk zance na gaskiya
Wasika zuwa ga shugaban ƙasa
Cikin masana'antar siyasa akwai mabiɗa nesa ta zo kusa
Wasika zuwa ga shugaban ƙasa
Cikin masana'anta ta waƙa akwai mabiɗa nesa ta zo kusa
[Verse 9]
Wasika zuwa ga shugaban ƙasa
Nufin su kawai wai shugaban ƙasa ya kame duk mariƙa kuɗin ƙasa
Wasika zuwa ga shugaban ƙasa
Bayan masu kudin ka ba su to in an kame su shin wa ya rasa?
Wasika zuwa ga shugaban ƙasa
Kun ga faɗan giwa guda biyu ciyawa ke wahala ta zam ƙasa
Wasika zuwa ga shugaban ƙasa
Mu roki Illahu ya ba su su ba mu mu bai wa na nesa mu bai wa na kusa
Wasika zuwa ga shugaban ƙasa
Ya Allah kare shugaban da duk bai da niyyan sace kuɗin ƙasa
[Verse 10]
Wasika zuwa ga shugaban ƙasa
Allah kare shugaba mai son gyaran tattalin arzikin ƙasa
Wasika zuwa ga shugaban ƙasa
Allah kare Naziru Sarkin Waƙa mai son ya ga ci gaban ƙasa
Wasika zuwa ga shugaban ƙasa
Ci gaban ƙasa
[Outro]
Allah ka kare musulmai da musulunci baki ɗaya, amin
Ubangiji Ka ba mu ikon gyarawa Ka sa mu zama masu gode maka, amin
Written by: Nazir M. Ahmad

