制作
作曲和作词
Auta mg boy
词曲作者
歌词
[Intro]
Mahamud Mg on the beat
[Verse 1]
Buga mini tambari zanyi tsokaci
Komai da lokaci, da gaske
Na ɗanyi tanadi, babu adadi
Don ƙara gargaɗi, a ɗauki
Idan duniya ashe sai da ɓandashe
Yau zamu raƙƙashe, da maggi
Duniyar nan ba mazauna bah
Wanda ka so bai maka ƙauna bah
Lahirar mu ita muke dubah
Masu dakon sharri bakuyi dace bah
Allah kare ni bazana butulce bah
Ni wanda ya soni da son shi nake kwana
[Verse 2]
Allah kaso mu
Komai ka bamu
Ba don halin mu
Kasa aji mu
A ƙaunace mu
Duk ayarin mu
Yau Rabbi gamu
Mun zo da kanmu
Fata kaji mu
[Verse 3]
Kare mu ga nuna zamba
Ga yan uwanmu
Bai zanma tsIra gare mu
Kowa zai so ka so shi
Yau rayuwa ce
A hakan muka tsinci kanmu
A ciki wasu zasu so mu
Don ƙudi garemu
Wasu kumah su aibata mu
[Verse 4]
Wasu zasuyi mana kyauta
Don suje su furta
Don cin fuska gare mu
Wasu kumah su so mu dan Allah
Su addu'a fah abun da zasu bamu
Mu wanan ya ishe mu
Tunda kunka so mu
Kuka ce kunji zaku yi mu
Duk sanda wanin mu ya fito
A haka zaku so shi
Ko ba komai garemu
Allah sarkin sarauta
Shi ke da iko
Ya aje wani wani ya ɗauka
[Verse 5]
Duk wani aiki da zakai
Toh ka kama Allah
Zakaga cigaba gare ka
Nima yau waƙa nake
A ciki anka sanni
Gashi ina daɗa ɗaukaka
Ba boka babu tsubbu
Ni na riƙe Allah
Allah shine mai duka
Allah kare mu ƴan tsiya
Masu ci da addini
Ka basu shiriya
[Verse 6]
Wasu masu baƙar aniya
Roƙona mai duka
Suma da ka basu shiriya
Duk wanda ya kama hassada
Roƙona mai duka
Shima a bashi shiriya
Duk wani mai kauce hanya
Allah ina bara
Da a bashi shiriya
[Verse 7]
Nima mai laifi ne
Allah na roƙe ka
Fatana a bani shiriya
Hanya ɗaya muyi ta tafiya
Mu zamo ɗaya babu wariya
Duka musulmi na duniya
Allah na roƙe ka
Ka bamu shiriya
Eh Allah a bamu shiriya
Written by: Auta mg boy

