音乐视频

音乐视频

制作

歌词

Ranar kuke jira yau gashi tazo
Nima da tamburana gani nazo
Ango nake yiwa shida amarya
Muyo rawa ta murna anyi aure
Ranar kuke jira yau gashi tazo
Muma da tamburanmu gamu munzo
Ango muke yiwa shida amarya
Muyo rawa ta murna anyi aure
Da fari nakira babban sarki
Shine yayo mutane da dawaki
Shi ya nufa nakai wanga mataki
Nayi fice cikin waka aiki
Nata gidiya ga Allah babu birki
Ina tayi a yau wasu na liki
Auren da ankayo ne da sadaki
Hakan sun ganshi tamkar a mafarki
A yau amarya zata tafi daki
Ibada can zakiyi
Ga ango kiyi kirki
Idan zakiyi girki
Ki girka da hannunki
Abinda yafiso shi zaki girka ke amarya
Ranar kuke jira yau gashi tazo
Muma da tamburanmu gamu munzo
Ango muke yiwa shida amarya
Muyo rawa ta murna anyi aure
Ranar da kuketa jira gata tazo
Dangi maza da mata duka sunzo
Wadansu 'yan Zaria wasu Gwarzo
Da ganin bikin ya wuce aci kanzo
Ga ruwan kudi na zuba sunyi tozo
Ango amarya dan ku kowa yazo
Farinciki mu nuna babu gizo
Dan kwalliyaku tayi kyau tayi cizo
Da aure, kun raya sunnar manzo
Ni kau addu'a a gareku na furzo
Dangi kuzo kuzo, kuzo
Musha rawa mu cashe da amarya
Ranar kuke jira yau gashi tazo
Muma da tamburanmu gamu munzo
Ango muke yiwa shida amarya
Muyo rawa ta murna anyi aure
Me yafi dadine a zaman tare, amana
Amarya da ango yadace ku kare hakkin juna
Idan an zauna a sama tarihi haka ya nuna
Idan kun saba kuyi sulhu karda ku yarda ku nuna
Makiya maso so sun ganku a rana (rana)
Kun tsone idonsu kunji batuna (batuna)
Allahu yakaimu watan watarana (rana)
Ku haifi diyanku ku sa masu suna (suna)
Allahu ya sa maku albarka
Dukanku dani danake waka
Iyaye nayi sam barka
Na doka kidana kun taka
Amarya taso (ehh)
Ke ango kiso
Haba
Ranar kuke jira yau gashi tazo
Muma da tamburanmu gamu munzo
Ango muke yiwa shida amarya
Muyo rawa ta murna anyi aure
Written by: Umar M Shareef
instagramSharePathic_arrow_out

Loading...