制作
作曲和作词
Auta mg boy
词曲作者
歌词
(AMG Boy Record)
Kina zuciyata, ban mance dake ba masoyiya
Ban mance dake ba sahiba
Cikin zuciya ta, ban mance dake ba
Cikin rayuwa ta, ban ga kamar yake ba
Har ina mance kaina in ban gan ki kusa dani ba
Kina zuciya ta, son ki yayi mini gata
Ina da burin dake zan kare rayuwa ta
Banga kowa ba sai ke
Domin ban mance dake ba habibiya
Ina nan dake, banga ranar rabo ba
Zo muyi zama inuwa daya, ba wai fushi zan dake ba
So ne yasa nayi ta bin ki, bawai rashin zuciya ba
A gan mu tare dake, ni a gare ni ba faduwa ba
Ruwan zuma soyayya
Ciki kaban na sauya
Nasha shi nayi ninkaya
Masoyiya, baga shi ba
Dani dake mutu ka raba, bazan yada ke
Kije dani, ki kaini duk inda zaki je ya masoyiya
Farin ciki, ki sani dadi zan ji a raina da zuciya
Na yarda so, yana shiga ya keta bargo da jijiya
Masoyiya, rike ni kam don rabo dake zani sha wuya
Girman ki ne, farin ciki zaya sa na ce miki sarauniya
Mai kyau na suffa, mai kyau na fata sunan ki ya zaga duniya
Nabi zuciya ta, so bai hana ni yin barci ba
Don ina dake ni, raina ba zai yi daci ba
Kin darawa mata, koda a fuska ba daya ba
Kin ji damuwa ta, kuma bai saki juya baya ba
Kyawun al'amari, shine ke sawa a zamo daya
Babu kamar ki garen, don kece kika ban goyon baya
Kece masoyiya, dake wanke zuciya
Kina sa ni dariya, don muyi zama na lafiya
Written by: Auta mg boy