制作

出演艺人
Auta mg boy
Auta mg boy
表演者
作曲和作词
Auta mg boy
Auta mg boy
词曲作者

歌词

(Da so samu)
AMG Boy Records
Burina
Burina
Burina
Zabi na
Zabi na
Zabi na ni kece
Burina
Burina
Burina
Zabi na
Zabi na
Zabi na ni kaine
Ni burina (kai ne)
Ni zabi na (kai ne)
Ni burina (kai ne)
Ni zabi na (kai ne)
(Eh mana)
Daga kallo daya duniya naji na kamu da soyayyah
Kece na aje raina baki da kishiya
Ciwon da yake damu na, na samo lafiya
Kece zabi na, zo nan zinariya
Kin ban soyayyah, soyayyah, soyayyah jigon rayuwa
Da gaske nake soyayyah, ta kama ni
Kaine ma'ajin sirri na, zo kusa ga ni
Da kai zan rayu a so, kama ni
Idan na gaza zan fadi, tarbe ni
Ka fidda ni cikin kunci so, mune a sahun farko
Zan baka kulawa, zan baka kulawa sosai
Dake na aminta da so, na aminta
Sautin ki shi nafi bukata, nafi bukata
Zan zo ta kusan ki na zauna, muyi hira
Akan ki idan na fusata, dukan sara
Mun tafi sosai munyi nisa, mun bar saura
Babu irin ki a duniya ta ke daya ce
Karda ka sa mini ciwon zuciya
In ka guje ni ranan sai na sha wuya
Yarda ta gare ka na bayar ba tsiya
Soyayyah nake maka tushen gaskiya
Muyi maja hadin kai tamkar tsintsiya
Ba wani, ba wani wanda nake so bayan kai na fada
Aah so yarda ne
Kece mai daki na, daki na
Na shirya
Mai boye sirri na, sirri na
Soyayyah
Zancen soyayyah ta
Ciwo na ka fama
Zan tado murya ta
Nima sai na rama
Zabi na kece wacce nake so in kaiwa dangi
Muyi zama dakai abadan-abadan ba zancen yaji
Written by: Auta mg boy
instagramSharePathic_arrow_out

Loading...