制作
歌词
Yazanyi ni ramlat, zuciya ta kaini ta barni
Tarkon dana fada na wuya wa zaya fiddo ni?
Ehh Ramlat ashe burin zuciya nakai mutum rami
Ta kaiki ta barki, yau ba tsuntsu bare tarko
Yau rijiyar daji aciki Ramlatu ta fada
Ba 'kugiya gefe waza yayi zabbari nata?
Ehh zuciya akwai sharri tasani ina tayin sa'ka
Na biyeta ta kaini wani rami gashi na apka
Mafuta garan kaine daya zaka iya ciran sarka
Nazo mudau hanya daya soyayya ta fishe ni
Yau rijiyar daji aciki Ramlatu ta fada
Ba 'kugiya gefe waza yayi zabbari nata?
Fanni naso Ramlat kince kowa da daidensa
Kinga kau idan na rufe baki ke zaki ban amsa
Kwalliya kudi na hada cikon burinki shi narasa
Tinda babu, na kasa kuma ya za'ayi ki aureni
Yau rijiyar daji aciki Ramlatu ta fada
Ba 'kugiya gefe waza yayi zabbari nata?
Ribar zaman duniya ka kasance dan masoyinka
Saukar ruwa na sama shike kawo tsirar shuka
Aike idan za'ayi mai kama da zuwa akan aika
Ma'anar ta na ganka nazo guna kazam tsani
Yau rijiyar daji aciki Ramlatu ta fada
Ba 'kugiya gefe waza yayi zabbari nata?
Yau rijiyar daji aciki Ramlatu ta fada
Ba 'kugiya gefe waza yayi zabbari nata?
Kiyi bincike karya da gaskiya nada banbanci
Na nura adalci yasa bawa yasam 'yanci
Zance da barkonci sune agareni sai naci
Ashe fa tun hanya tun farko shi ya kawoni
Yau rijiyar daji aciki Ramlatu ta fada
Ba 'kugiya gefe waza yayi zabbari nata?
Jan hankali da tunani na zasuyi amfani
Mu aje batun mota kafa ta ce ta kawo ni
Juyo kamun fara'a masoyina ka kalleni
Ina cikin ma wuyacin hali zo ka ceceni
Yau rijiyar daji aciki Ramlatu ta fada
Ba 'kugiya gefe waza yayi zabbari nata?
Komai nufin Allah ne ba wani abu mai tabbas
Ilimi akaina gunki hakan shine yayo cikas
Nidake a soyayya na kamu da fargaba da jiras
Kibi wanda ya dace bana burin ki zabeni
Yau rijiyar daji aciki Ramlatu ta fada
Ba 'kugiya gefe waza yayi zabbari nata?
Ya zanyi ni Ramlat zuciya ta kaini ta barni
Tarkon dana fada na wuya wa zaya fiddo ni?
Ehh Ramlat ashe burin zuciya nakai mutum rami
Ta kaiki ta barki yau ba tsuntsu bare tarko
Yau rijiyar daji aciki Ramlatu ta fada
Ba 'kugiya gefe waza yayi zabbari nata
Written by: Nura M. Inuwa