歌词
[Intro]
Musax
Musax beatz
[Verse 1]
Zahiri zaman duniya, ba ya yi mi ni daɗi
Idan babu ke cikin rayuwata
Eh, zaman duniya ba yai mi ni daɗi
Idan babu kai cikin rayuwata
[Verse 2]
Zo ki ji da ƙaunar ki za na mace cikin raina
Don ke ke saya mi ni duka sirrina
Kin sha tsangwama, zagi dalilina
Da in daina ganin ki gara in rasa idona
Ke ma kin sani
Ba yanzu ba tuntuni
[Verse 3]
Ke ce rayuwa
Rayuwa
Rayuwata
Mai ɓeben damuwa
Damuwa
Damuwa
Na gode
[Verse 4]
Na amince da wanda na sakarwa yardata
Zan kasance mai ba shi kulawa cikar gata
Shi kaɗai ne a zuciya ya zama mahangata
In zama matar sa shi na fi jira ina fata
[Verse 5]
Kai ma ka sani
Ba yanzu ba tuntuni
Ina son ka so na haƙiƙa Allah
Da in rasa ka gara na yo rashin daula
[Verse 6]
Soyayya da daɗi idan an soka
Zan fahari da yardar ki in kin ba ni
Kai ɗaya ne kalamanka
Kuma na ɗauka
Ban da wanin ka kai ne a kan mizani
[Verse 7]
Masu gani ku kalle mu to mun fara
So arziƙinmu mun sha wuya mun tara
Al'amari na so so a kaso da gadara
Ban da kamar yake na faɗa na ƙara
A cikin samari na kere sa'a
Tun da na samu mai yi mi ni ɗa'a
Ko a jikina ga masu mini ba'a
Sai ku ta yi ba za na bar abar ƙauna ba
[Verse 8]
Ɗan soyayya ai kai mi ni sata ni ma
Ban gane fari, ban gane baƙi har sai ka zo dama
Ka gaya mi ni mene ne sirrin don har ka samu gurin zama
Zuciyata ba wani tamkar ka
Ajiya kaimin kuma na dauka
Wallahi ina mugun son ka
Kana ta kula ni kamar ʼyar baby
Na gode ma
[Refrain]
Musax mix
Written by: Sadiq Saleh