制作
作曲和作词
Auta mg boy
词曲作者
歌词
[Intro]
AMG boy record
[Verse 1]
Alkawari damƙe ki riƙe
Kar kayi wasa karka sake
Jinki nake ƙaunar ki nake
A cikin raina ka laƙe
Zuciya begen ki take
Karka damu gidan ka nake
Soyayyah ce ta haɗa mu
Rabuwar mu akwai wahala
(Eh mana)
[Chorus]
Alkawari ki riƙe da ƙarfi
Son ki nake kiji ba da wai ba
Kaima alkawari ka riƙe da karfi
Son ka nake kaji ba da wai ba
Eh kaji ba da wai ba
[Verse 2]
Daga nesa nafara ganin ki
Na yaba da irin tafiyar ki
Kinyi kyau da ganin murmushin ki
Kika tara maza kallon ki
Ni na fisu nazo, zamu keta hazo
Da ganin ki nace ga kalata
Kinyi kala ta
[Verse 3]
Za'a wayi gari kaga munyi aure
Inda rabo mu rufe ta ƙyaure
Muyi haƙuri a zama mu daure
Har watarana muna a tare
Ka zama ni, na zama kai
Muyi rayuwar da ta burge kowa
Data burge kowa
[Verse 4]
Soyayyah ita ta haɗamu
Ko mutuwa ba zata raba mu
In dai tazo tare zata kai mu
Idan da hali rami ɗaya a haɗa mu
Dani dake, dani dake
In zamu rayu sai dai a inuwa ɗaya
[Verse 5]
Shiyasa don so bai da farashi
Balle a ce za'a taya shi
Ya wuce duk yanda ka san shi
Ko'a kala babu irin shi
Da kai zanje cikin dangi
Kai na zaɓa muyi rayuwa
Eh muyi rayuwa
Written by: Auta mg boy

