制作
出演艺人
Umar M Shareef
表演者
作曲和作词
Umar M Shareef
词曲作者
制作和工程
Aliyu Idris
后期制作工程师
歌词
Mallakin ki zan zamo bayan aure
Mallakin ka zan zamo bayan aure
Jarabawar son ki anyi min naci
Da soyayyar ki kullum nake barci
Da soyayyar ki nake cin abinci
Soyayyar ki ta cire kunci
Ka sani a zuciyar ka na zauna ciki
Ko mutuwa zata zo ta dauke ni ina ciki
Duk inda na gan ka ni bazan boye ba
In ka bar duniya bazan zauna ba
Nina fidda wacce nake so a zuciya
Idan zan fada maku sunan ta Mariya
Soyayyah ciki nayi dace a gaskiya
Na samu zabin Allah bani shan wuya
Masoyin ki nine fari
In same ki na cika buri
Kice nine bani inkari
Zuwa gun ki nayi da alkhairi
Na kawo kalaman soyayya ki jiya
Domin kiji dadi kiyi murna Mariya
Farin ciki kaine mai baiwa Mariya
Bakin ciki in nayi ka sakani dariya
Dana gane ka sai inji na zam sarauniya
Aure na dakai nasan bani shan wuya
A duba cikin kauyen nan gaba daya
Ba wacce ta dace masoyi ya Mariya
Hafeez gani nazo, bani in baki
Zabi kai na zabo miyo rayuwa
Nayi duba zuciya ta, babu kamar ki
Ke kadai ce kaf a mata, bata biyun ki
A guri na kinyi gata, ba'a taba ki
Ko'a bacci zani kwanta, sai da hoton ki
Kece damuwa ta, da so samu
A daura mana aure muyo rayuwa
Dukan lokacina, kaina baiwa
Rike min mana, ba adawa
Dakai zani zauna, koda yunwa
Zan sanya ka murna, babu rowa
Kaine garkuwa ta, ba mai damu
Yar lele ni na zamto cikin rayuwa
Hauwa-Hauwa Kulu yanmata adon gari
Hauwa, duk girman taro zana burge kowa
Ke nake wa soyayya ta
Ke naso ki zamto mata ta
Zana baki dukkanin gata
Guna baya ke a cikin yan mata
Mai rabo allurar cikin ruwa
Nine na zamo gwani na zarce wa tsara
Ni kai na ciro fili na gada
Mai kyan tafiya baya sanda
Tsafta bai sa kaya da dauda
Bana gajiya kai zana koda
Burin Hauwa Kulu shine kayi farin ciki
Zan zauna daman ka in dinga maka hira
Fati, Fatima autar mata
A raina babu yake har kullum
Kai na zaba samari kuyo hakuri
Na sanya ka cikin rai na baka wuri
Da ka nemi ka ganni zani zo da wuri
Cikin rayuwa ta ka wuce gishiri
Ni Fati zan yi wa mata kuri
Don masoyi na ya wuce kanwan lasa
Ni Zainabu Abu nake so, cikar burina
Bayan ke bani da kowa cikin kalbi na
Kyauta wacce zana fi so, ace mini gaka
Tafiya garin dani nafi so, aure dakin ka
Zance in za'ayi mini in so, a min maganar ka
Bacin rai abinda bana so, inji an kushe ka
A guna ka wuce kowa, kai baka da tamka
In zam maka mata kaiko miji babban burina
Ba rabuwa alkawarin ki na rike
Gamon jini so haduwar mu yayo dai-dai
Son ka ya shige a cikin rai ya kwanta
Shi ya zam silar samun lafiya ta
Da ke na so in kare a rayuwata
In zam mijin ki ke kuma ki zama mata
Zaman mu dole zai inganta
Tunda ba muyi wa juna mugunta
Kin zamo jini ni hanta
Rabuwar mu zaiyi wuya na furta
Farin ciki na sai karuwa yake
Ku duba fuska yanayi na haka zaku gani ma
A tsakanin mu babbar kalma ce gata
Gwanin dadi a gurin furtawa soyayya
Indai kasan gaskiya kar kayi karya
Ranar wanka cibiya bata buya
Indai na samo miya ban cin gaya
Soyayyah nan zan tsaya banyi baya
Kai zanyi jira duk daren dadewa
Batun aure in ba kaine ba ya zama labari
Kyawun ki shi ya saka ni na soki abar kauna ta
Kyan ki shi ya saka ni naso ki zamo mata ta
Kyawun ki wanda ya same ki shi ya zamo dan ganta
Kyawun ki wanda ya same ki yayi wa mazaje rata
Bawai kyawun da yake fuska ba
Bawai kyawun da yake fata ba
Bawai kyawun ki na kyan sura ba
Wannan kyawun nan da bai gogewa, halayya
Written by: Umar M Shareef