制作
作曲和作词
Thinking Mai Gashi
词曲作者
歌词
Abdul Tynking
Da M. Shareefi
Wannan naki ne mama
Rayuwa nayi nazari duk wanda ya zamto a raye
Wataran sai ya rasu ko yana so ko zai zub da hawaye
Duniya ba wajen zama ne ba aro aka bamu ba jaye-jaye
Mu rike Allah gwani mafita ne da manzo na fiyayye
Rayuwa ta sai a hankali
Na rashin mahaifya ta
Na zam kamar banda hankali
Ku dube ni bani da gata
Hakuri ya zama faralli
Ya Allah jikan mahaifiya ta
Wayyo (wayyo)
Wayyo, ya Allah jikan mahaifiya ta
إِنَّا ِلِلَّٰهِ وَإِنَّا إِلَيْهِ رَاجِعُونَ
Allah ya jikan ki mama
Don kin tafi wayyo ya zanyi
إِنَّا ِلِلَّٰهِ وَإِنَّا إِلَيْهِ رَاجِعُونَ
Allah ya jikan ki mama
Don kin tafi wayyo ya zanyi
Allah na gode
كُلُّ نَفْسٍ ذَآئِقَةُ الْمَوْت
Duk mai rai tillas ne ya mutu
Sai dai muyi dua'in neman hutu
Allah ya yafe mata
Kuka ka daina ka share hawaye aboki na
Dani da kai zata kan mu watan watarana
Ka zo mu roki Allah (eh)
In munyi sallah
Na san zaya kalla, ya Allah
Mutuwa nasan tana da zafi
Hakuri da za kayi shi yafi
Wanda ya mutu bazai dawo ba
Addu'a zamu shi zaya je gare ta, ya Allah
إِنَّا ِلِلَّٰهِ وَإِنَّا إِلَيْهِ رَاجِعُونَ
Allah ya jikan ki mama
Don kin tafi wayyo ya zanyi
Wayyo mama
Wayyo mama
Wayyo mama na
Wayyo mama na
Duk abinda nake so cikin duniyar nan mama tana bani
Yanzu bata nan yanzu na lalace dare da rana kullum tunani
Burin rayuwa in zauna da mahaifiya
Don ita ce garkuwa mai share duka damuwa
Wayyo mama
Wayyo mama
Wayyo mama na
Wayyo mama na
إِنَّا ِلِلَّٰهِ وَإِنَّا إِلَيْهِ رَاجِعُونَ
Allah ya jikan ki mama
Don kin tafi wayyo ya zanyi
(M. Shareef on the beat)
Written by: Thinking Mai Gashi

