歌词
Oh, oh
Yauwah, yauwah, yauwah
Larabeey
Ba sauki ai
Yanzu sai ka mutu
Za'a nuna ana son ka
Yanzu sai ka mutu
Za'a nuna an san ka
Tun kana raye, wasu zasu adana hoton ka
Tun kana raye, yakamata su nuna suna son ka
Ku nuna min soyayya san da nake raye
Ku nuna min soyayya san da nake raye
Mai taimako ka taimake ni san da nake raye
In zaka taimake ni yi san da nake raye
Ba sai na mutu ba
Ka fara posting dina
Ba sai na mutu ba
Ka fara zubda hawaye
Ba sai na mutu ba
Ka fara posting dina
Ba sai na mutu ba
Ka fara zubda hawaye
Sai ka mutu a fara kewan ka
Sai ka mutu a fara neman ka
Sai ka mutu a fara kuka
Wasu su yabe ka
Wasu kuma su zage ka
San da kake raye, ba mai share kukan ka
San da kake raye, ba mai duba halin ka
Ko ka nemi taimako, ba wani wanda zai baka
A boye alkhairi, a dinga bayyana aibin ka
Yane ne? (Duniya abar tsoro ce)
Yane ne? (Mutuwa rigar kowa ce)
Ku nuna min soyayya san da nake raye
Ku nuna min soyayya san da nake raye
Mai taimako ka taimake ni san da nake raye
In zaka taimake ni yi san da nake raye
Ba sai na mutu ba
Ka fara posting dina
Ba sai na mutu ba
Ka fara zubda hawaye
Ba sai na mutu ba
Ka fara posting dina
Ba sai na mutu ba
Ka fara zubda hawaye
(Ku mini addu'a, in na tafi yafi ku poster)
(Ku mini addu'a, in na mutu yafi poster)
Written by: Larabeey
