歌词
[Intro]
Salim Smart
It's Ahmerdy
[Verse 1]
Sonki ya yi mini tsiro
A zuci ya mi ni tarko
Ya hana ni sukuni ko ɗai
Ban ganin wata in ba ke ba
Ban zo da nufin wasa ba
Kowa ya taɓa ki ba zan iya ƙyalewa ba
[Verse 2]
So ya shiga zuci ya zauna
Ya sa ina ta sambatu
Ban ji ko an yi min magana
A zuci kin girma
Ba ni ʼyar dama
Son ki nake nema ki aminta da ni
[Chorus]
Soyayya (Soyayya)
Soyayya (Soyayya)
Soyayaya ta kama ni (Soyayya ta kama ni)
Soyayya (Soyayya)
Soyayya (Soyayya)
Soyayaya ta kama ni (Soyayya ta kama ni)
[Verse 3]
Babu rana, babu iska
Ba tsimi kuma ba dabara
In dai a kanki ne za ni jure garin nisa
Masoyiya, in dama zaki tausaya wa raina
Yana ta min zafi ki min agaji
[Verse 4]
Ki kwashe komai nawa ni ban damu ba
Kin mai da ni ɗan aike ni ban damu ba
Ki ba ni ʼyar dama
Na ba ki so ni ma
Da ni da ke soyayya ne za mu yi, ni Ahmerdy
[Bridge]
He hehe
Ah haha
Ah haha
Ah hahaha
[Verse 5]
Kina da kyawu ne
Kuma kyan na haƙiƙa ne
Masha Allah in dai na bar ki asara ne
[Verse 6]
Ni fa yanayinki ya min kama da Balarabiya
A'a yanayinki ya min kama da na India
A'a yanayinki ya min kama da Baturiya
Yaya zan yi ne in kwatanta kyawunki ne zinariya?
[Chorus]
Soyayya (Soyayya)
Soyayya (Soyayya)
Soyayaya ta kama ni
Soyayya (Soyayya)
Soyayya (Soyayya)
Soyayaya ta kama ni