制作
作曲和作词
abdulkadir tajuddeen
词曲作者
歌词
AD music studio
Wai yaushe, yaushe ne?
Yaushe idanuna?
Za suga mai so na
Wacce nake kauna
A dare rana
Wai yaushe idanuna?
Za suga mai so na
A son ta nake kwana
A dare rana
Da zuciya da raina na bar maka su suma
Da hankali da jina na baka su suma
Abunda ke yawo a jinina duk na bar ma
Komai ka so gare ni zanyi shi jikina na kyarma
Ni ce masoyiyarka 'yar asali
Juyo ka ganni na sha kwalli
Ina gudun in barka wani hali
Ni zan cika alkawari
Zan zamo diya ta gari
Mu cike da tasiri
Ba zana baka kunya ba
Wai yaushe idanuna?
Za su ga mai so na
Da son sa nake kwana
A dare rana
Wai yaushe idanuna?
Za su ga mai so na
A son sa nake kwana
A dare rana
Ina taji cikin raina
Zamu zauna wata rana
Zan rayu da mai so na
A nan da can Insha Allah
Mu gasgata tauhidi
Samu rashi duka na Allah ne
Rayuwa tai dadi yau gobe kunci duka na Allah ne
Wanda ke cinye jarabawa
Shine mai imani
Mai imani
Wannan ya yarda da Allah ne
Zan cika maki alkawari
Zan zamo mutum na gari
Ciki da tasiri
Baza na baki kunya ba
Written by: abdulkadir tajuddeen