歌词
(C One)
(AD Music Studio)
Mu amala
Mu amala
Mu amala
(C One Producer)
Ki bani lokacin ki, ko zana rayu a duniya
Ki bani tabbacin zama na dake, kin ji masoyiya?
Nidai-nidai-nidai nake son ki, na fi kowa jin ki a zuciya
Wallahi nayi arangama da son ki ne a birnin taraiya
Ina ta yi miki magana kina ta sauri kin ki ki waiwaya
Ko zana rasa komai a rayuwa ni dai ki yarda ni da ke muyi masoyiya
Nayi ta duba irin ki ko zana dace a social media
Sai gashi ban dace ba don ke daban kike ba irin ki ko daya
A kan ki zan saka cigiya, sai dai bani da shaida ko daya
Da son ki zan iya mutuwa, sai dai ina da dalilin rayuwa
Wayyo ni, wayyo duniya masoyiya ta mini mugun mamaya
Abinda ban taba sawa kai na ba gashi yau ina tayin bibiya
Kowa ya rayu yacce yake so, ammah ni na kasa bai daya
Na so abinda ban san ya zata soni ba, soyayyar zuciya
Allah yasan na so ki tamkar in ce rai gare ni a duniya
Nima nasan ka so ta tamkar ka ce ran ka gaba daya
Gashi ko kallon ka ba tayi bare ma tayi maka dariya
Don Allah share ta kaji kar ka kamu da ciwon zuciya
Tun da ba takai take ba ka daure ka mance mu barta da duniya
Ni zana so ka ko baka sona mu rayu gaba daya, kaji?
Ai sai dai ki so shi ke
Dama ba tsaran mu daya ba ni dake
Ka duba ta kadan ai tafi rake
Toh haka yake ko tsakanin mu ni da ke
Zaren ba kalar yadin ba muke
Ko a bangaren flows na bambanta dake
Ki so shi dama daidai dake yake
Na barku lafiya ku ci soyayya
(C One mix)
Written by: Abdul D One


