積分

演出藝人
Nazir M Ahmad Sarkin Waka
Nazir M Ahmad Sarkin Waka
演出者
詞曲
Nazir M. Ahmad
Nazir M. Ahmad
詞曲創作

歌詞

[Verse 1]
Wakilin Minna, babban sagi mai Minna
Ina damina uwar albarka Yakubun Minna
Allah ne yai ma dafi kai ma sai kai dafi hakimin Minna
An ma wakilin Minna Yakubu Abubakar (Wakilin Minna)
[Verse 2]
Babban sagi mai Minna
Ina damina uwar albarka Yakubun Minna
Allah ne yai ma dafi kai ma sai kai dafi hakimin Minna
An ma wakilin Minna Yakubu Abubakar
[Verse 3]
Wakilin Minna babban sagi dan Abubakar farin nera
Wakilin Minna, babban sagi mai Minna
Ina damina uwar albarka Yakubun Minna
Allah ne yai ma dafi kai ma sai kai dafi hakimin Minna
An ma wakilin Minna Yakubu Abubakar
[Verse 4]
Ilahi Allah komai muke farko mun saka
Mun daukaka da ikon Allah
Mun shahara da kere sa a
Mun tafiya da kamun kafa
Mun addu'a, muna ta addu'a
Mun yi shiri muna godiya
Allahumma salli ala rasulullahi
[Verse 5]
Wakilin Minna, babban sagi mai Minna
Ina damina uwar albarka Yakubun Minna
Allah ne yai ma dafi kai ma sai kai dafi hakimin Minna
An ma wakilin Minna Yakubu Abubakar
Wakilin Minna, Yakubu Abubakar Minna
[Verse 6]
Babban Sagi mai harka
Turmi ka shanye daka
Zaki ka sa a yi da'a
Mun dan matso mu yabe ka
Ga tambura mun doka
Manya suna zancenka
Haske cikin allonka
[Verse 7]
Amma dai alhaji, amma dai alhaji sauki cikin aikenka
Gun yafiya an sanka
Tausayi da sa albarka
Hakiminmu ya daukaka
Abin da kayyi na kirki alhaji ya bi ka har karshenka
[Verse 8]
Ina ma a ce mun san ka
Mu yi ta zazzago zancenka
Amma a sannu, amma a sannu mun zo mu gan ka mu san ka
Mu gan ka ga hakimai amma adonka daban ne
Ramin kura sai dan ta
Wakili ka cancanta
[Verse 9]
Ado an yi shi, ado an yi shi, ado cikin kasaita
Ga malaman ga sarakuna, ga hakiman duk nai wa waka
Eh an dau ado, dada an dau ado amma adon wakili daban ne
Ehhn! Shin ko kun gano dawisu
Dawisu ya bace taron nan
An gama an rufe zancen nan
Duk mai ado ta shafe shi
Yai mai wuri ya dauke shi
[Verse 10]
Mu hakiminmu dan wanka ne
Dan dakata ka ji alkyabbarsa
Dole ta sai gida da motarka
In ma dan wuri takalmansa sai ma su sai wurin sana'arka
Shi nas saka idan ya fito waje
Sai ka ji al'umma suna dawisu
[Verse 11]
Na walwali maliya ka fi su
An tara al'umma ka danne su
Ka zama damina mai inganci
Mushen gizaka baya lalaci
Ka bai wa 'yan gida ka bai daji
Alhaji al'umma duk sun gode
Sun ce idan dawar nan tai nama sai su samu fili sun huta
Kai kake mu su har 'ya'yansu
[Verse 12]
Wane rago (Da rigar saki)
Wakilin Minna bangon jingina
Sai yad dada da tsoron Allah
Wane rago da rigar saki
Kowat taba ka sai mun taba shi
Nan ba shi ba mu tsoro wallah
[Verse 13]
Wakili dai maso mai sallah
Da ikon Allah
Wakili ba dai mutum ba
Wakili ba dai mutum ba
Eh mutum ba zai wa mutum ba
Uhm don damisa ta fi doki
[Verse 14]
Eh! Sarkin yawa ya ci daki
Wakili ba dai mutum ba sai dai Allah
Idan hakimai suna yawo
In sun taho cikin iko
In ka gano wakilin Minna daban za ka gan shi don ya fi su
Ado garai kamar dawisu
Ga kwarjininsa duk ya fi su
[Verse 15]
Taro ana ta taro ana nadi na wakilin Minna Yakubu
Taro ana ta taro ana nadi na wakilin Minna Yakubu
Zance ina ta zance ina ta zance cikin kida dan baba
Taro ana ta taro ana ta taro ina gano su na baba
Taro ana ta taro ana nadi na wakilin Minna Yakubu
[Verse 16]
Na hangi sarakuna, sannan manya na al'uma
Rannan na hangi maluma
Sannan manyan cikin kasa
Sun zo domin ana nadin Yakubu
[Verse 17]
Taro ana ta taro ana nadi na wakilin Minna Yakubu
Da ne ga janaral Abdussalami Abubakar Yakubu
Taro ana ta taro ana nadi na wakilin Minna Yakubu
Dan marigayi dai Abubakar wakilin Minna nan yai gado
Taro ana ta taro ana nadi na wakilin Minna Yakubu
[Verse 18]
Dan hajiya Hauwa Amma, addu'arsu duk ta bi ka
Taro ana ta taro ana nadi na wakilin Minna Yakubu
Dan justice Fati Lami Abubakar muna gaishe ku
Taro ana ta taro ana nadi na wakilin Minna Yakubu
Dan uwan alhaji Aminu Abubakar tafiya mazajen aiki
Taro ana ta taro ana nadi na wakilin Minna Yakubu
[Verse 19]
Dan uwan janaral Jibril Abubakar JT tafiya san aiki
Taro ana ta taro ana nadi na wakilin Minna Yakubu
Dan uwan alhaji Ummaru a gai da shi kun ga garkuwar MIinna na mu
Taro ana ta taro ana nadi na wakilin Minna Yakubu
Dan uwan alhaji Ado Abubakar lafiyarka dan limami
Taro ana ta taro ana nadi na wakilin Minna Yakubu
[Verse 20]
Dan uwan alhaji Jibril Sulaimanu ajiyar mutanen kirki
Taro ana ta taro ana nadi na wakilin Minna Yakubu
Dan uwan hajiya Asabe ana ta taro muna ta sannu da aiki
Taro ana ta taro ana nadi na wakilin Minna Yakubu
Dan uwan hajiya Hauwa Ladiyo mu dai muna yaba maka zaki
Taro ana ta taro ana nadi na wakilin Minna Yakubu
[Verse 21]
Dan uwa hajiya Aisha Abubakar muna ta sannu da yaki
Taro ana ta taro ana nadi na wakilin Minna Yakubu
Dan uwan hajiya Ladidi Ammada Minna masoyin Allah
Taro ana ta taro ana nadi na wakilin Minna Yakubu
Taro ana ta taro ga sarakai suna ta kai wa da kawowa
Taro ana ta taro ana nadi na wakilin Minna Yakubu
Taro ana ta taro na ga abokai suna ta sannu da aiki
Taro ana ta taro ana nadi na wakilin Minna Yakubu
Allah ya sa mu dace, Amin
Written by: Nazir M. Ahmad
instagramSharePathic_arrow_out

Loading...