Music Video
Music Video
Credits
PERFORMING ARTISTS
Nazir M Ahmad Sarkin Waka
Performer
COMPOSITION & LYRICS
Nazir M. Ahmad
Songwriter
Lyrics
Zuciya ba ta mutum ba
Ba ƙashi kuma ba ta da girma
Zuciya ba ta mutum ba
Ba ƙashi kuma ba ta da girma
Idan na tuna da masoyi sai in ji taura na taɓa ƙara
Idan na tuna da masoyi sai in ji ƙwalla na ta kwarara
Idan na tuna ka masoyi sai in ji tamkar in saka ƙara
Idan an ce in bar ka sai in ji mutuwa ba mu da tazara
Na yi kewa, na yi kewa, na yi kewar mai mini hira
Na yi kewa, na yi kewa, na yi kewar mai mini hira
Na yi kewar ɗan Amina, ɗan kyakkyawa, masoyina
Ka yi nisa, ka yi nisa, ka yi nisa malamina
Da ace wannan fa zai kai inda ruhin masoyina
Da anan zan bashi labarai na birnin zuciyana
Labarin masoyiya
Labarin masoyiya
Labarin masoyiya, ban ji yadda aka kai kika kwana ba
Labarin masoyiya, ban ga wacce ta kai ki a guna ba
Labarin masoyiya, ban ga wacce dai ta shige mini zuciya
Ta samu gurin zama, tai zamanta ta tsaru da kwalliya
Kin ɗau hankalina
Kin saren jikina
Ni duk dukiyata
Ke nai wa dashena
Maraba da rayuwa wadda ke ta haɗa mini ƙaruwa
Maraba da ɗan ruwa wanda shi naka sha in hau rawa
Maraba da ƙaruwa wacce dai ta tsayar mini damuwa
A zaune da kwanciya sai in gan ki kina mini dariya
Na damu da jaruma sai ta damu da ni mu yi rayuwa
Na ɗauki abin kiɗa, zan kiɗa sai in mata 'yar rawa
Idan sonta rijiya ne, ina jin ina ƙasa na nutse
Ku bani abin zama, ban san sanda zan bar ta in zo ni ba
Labarin masoyina
Labarin masoyina
Labarin masoyina, ban ji yadda aka yi ka kwana ba
Labarin masoyina, ban ga wanda ya kai shi a guna ba
Labarin masoyina, wanda dai ya shige mini zuciya
Ya samu gurin zama, yai zamansa ya tsaru da kwalliya
Labarina
So ni ƙarshen sonka masoyi, don shi fa so ya tsarmu da tsuntsu
Tunda dai na kamu da sonka ba yadda zan na iyai maka tutsu
Na yi kewa, na yi kewa, na yi kewar mai mini hira
Na yi kewa, na yi kewa, na yi kewar mai mini hira
Na yi kewa, na yi kewa, na yi kewar mai mini hira
Na yi kewa, na yi kewa, na yi kewar mai mini hira
Allah Ya sa mu dace Amin
Written by: Nazir M. Ahmad