Credits
PERFORMING ARTISTS
Nazir M Ahmad Sarkin Waka
Performer
COMPOSITION & LYRICS
Nazir M. Ahmad
Songwriter
Lyrics
Ba'a cinye Toron Giwa
Giwa da ranta to sai dai kallo
Sarkin Kanonmu mai alfarma
Sarkin Zaria na nan shi ma
Sarkin Musulmi mai ɗumbin daraja
Sarakuna iyayen kowa ne
Ba'a cinye Toron Giwa
Giwa da ranta to sai dai kallo
Sarkin Kanonmu mai alfarma
Sarkin Zaria na nan shima (Gaishe ku)
Sarkin musulmi mai ɗumbin daraja (A'a)
Sarakuna iyayen kowa ne
Kare da kai bakwai sai kallo
Ita ƙarya fure take ba 'ya'ya
Kamar mutum tana nan daidai
Ko yai shiga yana nan ɗai-ɗai
Kare da kai bakwai ko da ɗa ne
Da ka gane shi ka san aljan ne
Zaki cikin awakai sarki
Kai kura da akuya sai dai kallo
Ruɓurɓusa take ban taushi
Mai akuyar yana jin haushi
Ya labe da adda nan gefe
Yana jiranta ta kai ya kar ta
A gafara nace ga kyarkeci
Wannan batunsa na can baya
Girmansa ne kawai ɗan banza
Ga kwarjini kamar wata gabza
Ko akuya tana yi mai waigi
Da ta biyo shi sai dai yats tsere
Bara in waiwaya baya
In duba rayuwar baya
In binciko hirar wata gawa
Sarki tura fa ta kai bango (Iye)
Ka saka mu a loko
Zance kake kamar wani soko
Hirar dabba muke yi ko waka
Hirar Kanon kuke so ko Zazzau
Ka kyale Baba Bakwa ɗan Zazzau
Da baya noma komai sai doya
Idan ya ji ku kun san zai rama
Eh ko da ya jimu ba zai ce shi ne ba
Ba shi so a ce mai ɗan Zazzau
Kuna nufin yana kalan dangi
Idan ya je ga boda yah haura (Iye)
In ya yi Niger
An ka ce Kano ne ko Zazzau
Sai yace Kanon nan ta fi su (Gaske)
Ko manyansu don ba su so a gane sunansu (Ku ce da su)
To mu mun san su
Ya ake ana gane su
Mallam shigarsu mai ban tsoro ce (Ashe)
In sarki ne in ya taho kamar wani gwanki ne (Gaske)
Sarkin Zazzau in ya shigo kamar wani Giwa ne (Gaishe ku)
A fagen mulki al'amuransa tamkar rana ne (Haka ne uhm)
In ta haska duk duniyar ga kowa ya gane (Iye)
Al'adunsu kamar ace mutanen farko ne (A'a)
Sarkin Zazzau ga tambura yau mun doka (Hmm)
Naziru ne sarkin waƙa (Gaishe ku)
Ya shigo a Zaria gaisheka (Ehn hm)
Lafiya zaki ko wat taɓa ka yau sai ya koka
Sarkin Musulmi na Sokoto mai ado mai makaman yin yaƙi
Sarkin Musulmi na Sokoto mai ado mai makaman yin yaƙi
In gaida Sarkin Musulmi na Sokoto mai ado mai makaman yan yaƙi
Sarkin Musulmi na Sokoto mai ado mai makaman yan yaƙi
Eh gaisuwa ga babban dutse karyar su kwai su kawo ma raini
Sarkin Musulmi na Sokoto mai ado mai makaman yin yaƙi
Gaisuwa ga babban jeji ko wab bace ciki sai dai ihu
Sarkin Musulmi na Sokoto mai ado mai makaman yin yaƙi
Eh gaisuwa ga babban sarki wanda in ya tashi kowa zai miƙe
Sarkin Musulmi na Sokoto mai ado mai makaman yin yaƙi
Eh gaisuwa ga sahun Giwa taken su wa na mai tsoron aiki
Sarkin Musulmi na Sokoto mai ado mai makaman yin yaƙi
Eh gaisuwa ga babbar fada baban sarakuna 'ya'yan kirki
Sarkin Musulmi na Sokoto mai ado mai makaman yin yaƙi
Sarkin Musulmi Nazir sarkin waƙa ne yake yi ma baiti
Sarkin Musulmi na Sokoto mai ado mai makaman yin yaƙi
Su dawisu masu ado
Sarkin garinmu mai kyan zamani
A Kanon dabo
Mu dai garinmu akwai ban mamaki
Lafiya iska
Kowa ya kewaya zai sameka
Lafiya tarko
Ko wash shigo ka zai sha mamaki
Ka ga dutsen murhu
Sai an aje ka ne za a yi ɗori
Sasarin alkali
Dukkan mazan gari na tsoron ka
Mai ado mai tsari
Ɗawisu 'yan gari na kaunar ka
Sarkin Dabo
Mai martaba da alfarma
Mai wa ɗiyansa ne hidima
Mu dai sarakuna yau mun samu
Sarakuna iyayen kowa
Mu daki tamburan sarki Nazbi
Sarkin waƙar da duk duniya duk an san shi
Mai kayan yaƙin da duk duniya ke tsoron shi
Mai girma Nazbi jama'arka na nan damanka
Shiga da kanka mai komai Naira
Sarkin waka duk duniya na gaishe ka
Mu daki tamburan sarki Nazbi
An baku mota yara
Sarkin waƙar da duk duniya duk an san shi (Hmm)
Mai kayan yaƙin da duk duniya ke tsoron shi (Gaishe ku)
Mai girma nazbi jama'arka na nan damanka
Shiga da kanka mai komai naira (Ga miliyan biyu ku sha mai)
Sarkin waƙa a duk duniya na gaishe ka
Ga sarkin waƙa (Wanne)
Baban Islama (Gaske)
Mai haƙora na azurfa maƙogaronsa tamkar zinari (Gaskiya ne)
Fannin waƙa (Hmm)
Kun ga shi ya gawurta
In kana jin muryarsa sai kace kana susar kunne (Sarki yana ji)
Don daɗinta (Ashe)
Shi ya gawurta
Al'amuransa sai ikon Allah (Ashe kai ma sarki ta ka za ta yi kyau)
Lafiya na Nazbi
Sannu baban Islama (An hada maku da dawakai)
Buhun kaya sam ba'a ciko
In an cika ka kuma ba'a danni (Gaskiya ne)
In an danna mutum ya soke hannunsa (Gaskiya ne)
Ba wanda ya tsaya ma sai Allah balle mutum yace sai ya kar ka
Sarki ya gode
Babu mai ma sai Allah balle mutum yace yau ya daina
Gaskiya ne
Allah ka kyautata karshenmu, Ameeeeen
Written by: Nazir M. Ahmad