Top Songs By Isah Ayagi
Similar Songs
Credits
PERFORMING ARTISTS
Isah Ayagi
Performer
COMPOSITION & LYRICS
Isah Ayagi
Songwriter
Lyrics
Na fahimta idan muna tare
Lokaci yafi sauri
Ai idan mun rabo
Ina rayuwa cikin tari-tari
Ban fahimtar ku wani zance
Sai an yi mini kwari-kwari
Ke kadai ce kika zuwar min
Cikin tinanin mafari
Kaddara ta dafare ni
A sanki fili da sirri
Yau idan kinka bar ni
Ni zanayo kiran ajalina
(Beat Alix production)
Zuciyata na baki
Domin kina da babban masauki
Nayi niyar auren ki
Ko zana badda duk yan kudina
(Zuciyata)
(Ke kadai ce)
So farar damisa
A chan nisa nada dadi na kallo
Tunda dukan matsin shi
Nan zaya sauya sunanka dolo
Dukanin hakurinka sai ya kure ka
Kazam mai hakilo
Gashi tafin hanu
Baya kare rana inda bulo
So ruwan damina
Ba mai iya tare shi
In har ya balo
Lokaci dai yake shiga
Gun fitar sa sai anji kuna
Ah-hh-hh-ah-ah-ah
Ko ina nake
Ko a mene nake zuciya bata tsira
Naga karyar gudu a daji
Kare idan yaga kura
Zuciya ta rufe da so
Na duhu bai gane harara
Babu zahiri idan dai kare
Ya mace saura
Na rika na kware a so
Yanzu banda sauran dabara
Har idan zana ganki
Toh zana mance duk matsayina
Ah-hh-hh-ah-ah-ah
Tabbatar min da so cikin zuciyar ki
Ko naji sauki
Ya ki kashe min wutar dake ruruwa
Tabar yin hayaki
Sauya min ruwan madaci
Kiban zuma tafi zaki
Takaita nisan mu banda burin
Ki dauke halina naki
Kadaita taraiyar mu zaman lafiya
So yafi yaki
Dan ni ko dan gidan ku
Kishi nake idan zaku gana
Na fahimta idan muna tare
Lokaci yafi sauri
Ai idan mun rabo
Ina rayuwa cikin tari-tari
Ban fahimtar ku wani zance
Sai an yi mini kwari-kwari
Ke kadai ce kika zuwar min
Cikin tinanin mafari
Kaddara ta dafare ni
A sanki fili da sirri
Yau idan kinka bar ni
Ni zanayo kiran ajalina
Writer(s): Isah Ayagi
Lyrics powered by www.musixmatch.com