Lyrics
Tani da Manu
Ah-ah ba tambaya
Da an ganemu ah-ah
Za a gane masoya ne
Tani da Manu
Ah-ah ba tambaya
Da an ganemu ah-ah
Za a gane masoya ne
Kyakkyawa labari ni ne ke tsa tsarawa
Ke kuma daliba ta da na fada sai ki kwashewa
Juma'a mai alkhairi da Larabar ta ake ganewa
A kira ni da sunan ki
A ko ina zani amsawa
Hannuwan ki a bude suke
Baki kama da masu rowa
Zan kira ki da sunan ki
Tani ta Manu ki amsawa
Gobe da labari
Bazan boye ba
Wace nake kauna Tani baza ta gujen ba
Ko kayi sallama ga malami na mai koyarwa
Nice daliba Tanin ka wacce kake nunawa
Alfahari na kai ne
Batun ka bana son dainawa
In munci kwalliya dani da kai ba mai kushewa
Dukka mai kudurin ya rabamu
Ni da kai sai yai kokawa
Zuciya tai ambato shigar gidan ka take furtawa
Wane da kai zanyo ado
In cincire
Sarki kai ne mai gida na sai na fada
Hanya ta ba gargada
Ki biyo zata kai ki cikin gida
A daki nai maki shimfida dan ki huta kinji ta mai gida
Jirgi zana siya maki na soyayya komai tsada
Shi koh wanda yake shirin miki kallo zai sha sanda
In kin dau hannu zama na dake bazai kare ba
Sannu a sannu kulawa ta so baza na ki yi ba
Mai raba kauna baiyi ba
So haduwar tsokar jini bai zo da fada ba
Tani da Manu
Ah-ah ba tambaya
Da an ganemu ah-ah
Za a gane masoya ne
Fito filin ga mu kewaya
Mu nuna kauna
Masoyin gaskiya dan amana
Baka gudu na
Ina nan tare da kai
Ko-ko ana bugu na
Manu akwai kishi haka nace iya sani na
Banda kamar ka a rai
Kai ne ka zama ginshiki na
Ruwa in yai zafi ba a shiga ciki a zauna
Toh haka soyayyar ta kai
A zuciya
Ni na fada ban yada kai
Ko badan bada da
Tani da Manu
Ah-ah ba tambaya
Da an ganemu ah-ah
Za a gane masoya ne
Tani da Manu
Ah-ah ba tambaya
Da an ganemu ah-ah
Za a gane masoya ne
Written by: Abdul D One