Credits

COMPOSITION & LYRICS
Farfesan waka Sulaiman
Farfesan waka Sulaiman
Songwriter

Lyrics

Azzalimi ba zai zam adali ba
Makaryaci ba zai girman kwarai ba
Marowaci ba zai kyautar yabo ba
Mai kwadayi ba zai taba zuciya ba
Mai gaskiya ba zai cutar da mu ba
Munafuki ba zai zam akili ba
Mazambaci ba zai zam amini ba
Dan Ahmadu ba zai bar tsokaci ba
Maketaci ba zai iya tausayi ba
Mugu ba zai ji dadin taimako ba
Duk mai jiran yabo bai aikata ba
Rashawa gare ka ko ba a ce da kai ba
Mai illimi da jahillai ba sai kama ba
Aikin kwarai ba zai tabar da kai ba
Banbarakwai adon da ba ayyi kyau ba
Talakan da ke da izza ba yabo ba
Kyale tsugul idan ba a sa da kai ba
Dukkan kashin da ba kai ba rabo ba
Farfesan Waka ba gwani ba
Koyo ba shi kaskantar da ni ba
Dirka da ginshiki ba kishiya ba
Boto ba zai ji haushin ko guda ba
Wasa farin girki ne al'umma zancen ma ba a fara ba wannan kasa
Wane ne ba shi ne ba wannan kasa ban san wa zan dauka ba
In wannan Nigeria ce wannan kasa mamaki bai kare ba wannan kasa
Gautan duka ba ja ne ba al'umma ba zan ce masa kore ba
Kowanne ma ja ne ai don son rai shi anka bi ba Allah ba
Ba tallakka ba ba malam ba wayyo ba attajirin siyasa ba
Ba mazanmu ba ba matan ba kai kai kai ba yaro ba wala babba wannan kasa
Kasuwanci da gurin bauta wassu suke ba su damu a yo sallah ba
Mabiyansu suna tata amma su ba su san da suna wahala ba
In dai maganar Naira ce duk matsalar da ta zo ba sa sauya ba
Maasallaci jarisu mazanbata ba su je sun yi sana'a ba wannan kasa
Sai ka ga coci ana sa'insa da su fasto faada na karyar wahayi
Mabiyansu kamar sa zautu sun dage sun bar su suna ta bulayi
Da yawansu barayi ne ma da mamura suka addini tamkar yayi
Sun boye ba su boye ba yan damfara ba ku girmama addini ba wanan kasa
Yau ni maganata zan yi Farfesa mai tsoro maza bar guna
Zan kwance zare da abawa gyara zama na gajji da yankan kauna
Duka wa-ka-ci ka-tashin nan shashancin da muke yi zan tattona
Hauma-hauma harrigido rubibi rudu shi mun ka fi nunawa wannan kasa
Ka ga sarki ya kai sarki ga rawani wai gwamna yake jin tsoro
Ga mulki ga ikon nan gargajiyarmu bature ya kai kwaro
Su kakkafa duk tsarinsu mu tsarinmu ya koma sai sauraro
Sarki mai darajar karshe su ka maishe shi kamar wani dambun barje wannan kasa
Yan siyasa wasu sakarkar wadanda ba sa cin zabe ko kyauta
In sun gaza samin zabe sai su fake da kabilanci don cuta
Ko su sarfaci addinin su sa ana ta zubar da jinin bayi mas bauta
Su ke saro tarzo ma har su kasa domin samin ribarta wannan kasa.
A kasar nan ka ga matashi ya zaga neman mace mai 'yar kumba
Kumabar susa itta mana kwadayaye wai shi ba zai wahala ba
Akwadaye ba zai gane ba sangarta Dangoma ba zai yafe ba
Ka ga wassu suna halin lau suna bara ba su damu su yo aiki ba wannan kasa.
Kun san tafiyar shanshani kwai zarya ban fadi ba ban kasa ba
Ka ga tsoho tinkis-tinkis yai fyade karamar 'ya bai duba ba
Ko kumma a yanke sassan wasu yaran ba kaa ki ka ce tsafi ba
In dai duka Nigeria lallai ko mamaki bai karewa wannan kasa
Mai mulki ya yi gazawa ya kasa ba ce massa ya kauce ba
Bai san ya zai mulkin ba ya rude ba a ce sauka ka bar gun ba
Jama'a na neman ceto sun zauna ba su san ma me za sui ba
Talakawa gugan yasa 'yar kuka a makaifa kuke tun ran nan wannan kasa
To wai wa ma zan zaba ga mata na kasshe mazajen kulle
Kishi ne ko kuma hauka ko sakaki na mazajen ya ka kalle
Rikicinmu a da na saki ne da yai yawa yanzu ko kisa dan makale
In so daga soyayya ne ya rikide sunansa ba zan furta ba wannan kasa
Ku biyo ku ji lissafi gun Farfesa lalata ba ta kare ba
Layi sam'bal ran zabe mun jeri ko an gaji ba a koma ba
An sha rana an koku an dage sai wane ba ai fashi ba
Wannan ce ranar zabe ran 'yanci sannan kuma ranar bauta wannan kasa
Ya tai karaga ya zauna ya harde mu ne farko kangewa
Mota tintak tai dund'um ta yi duhu ya bar mu cikin tabewa
In zai keto yankinsa tsakar dare duka kun gaji kun kwantawa
Layin da akai ran zabe shi zai ai a gidansa ana dakon sa wannan kasa
An tadiye lantarkinka ba haske an kawo inji ka saya
Ita harbitsilar 'yan gwangwan ta fi haka kai dai ka natse ko ya ya
Za ka gane batun yaron nan Farfesa in kwai hikima a koya
Lantarkin bai zauna ba rana Fela ya taba yin zancen wannan kasa
Da na kalli refineries du na kasar na san magana ce kwance
Ya mu da muke ta hako mai danye cakal sai a kai waje a tattace
Gaarinka da za ka yi kulli sai ka kai wa makota sun ma bakace
An shirya batun girkin nan ko ko dai an fi gano a auno dusa ina kasa
An cefanar da lardin nan an kare la'ada ce ba ta kare ba
Wani likkita bai aikinshi yai private can zai tafi bai zo nan ba
Bai sauke farillar kai ba ya mance hakki nai bai sauke ba
Karshen magana shi kenan an kare ba a gyara takin farce ba wannan kasa
Wasu sun dauki kiran a rabe wannan kasa wai zama haka bai dace ba
Wasu baki suke furtawa wasu aikin da suke bai boye ba
In ana fadan kabilanci a kasuwa to maye haka ba gilli ba
Da wuya haka ke burge mu amma su kullun shi ne burinsu raba kasa
Ban tashi da mamaki ba wata kasa da tsaro bai zam tilas ba
Ko kana mota babu tsaro ko jirgi a gida ba ka san tabbas ba
Ba a ganganci da tsaro don rayuka ba su dace da siyasa ba
Ka ga fillo yana kiyonshi ya daina garkuwa ta fi masa kenan wannan kasa
A cikinta idan kai cuta kai funfuris duka kotu ta zam yaronka
Ko ka ci amanar jama'a sama da fadi ka cika lalitarka
In ka iya kale lulaye ka mika wa zai ji da labarinka
In gobe ta zo an manta sai ka fito baka-baka kau toro wannan kasa
Kai har wata karya na sani mai haushi don dakile aikin zamba
Yanzu za mu ji zance ga shi an ta'annati a zatonka ba yafe ba
Yau gobe walewallewa shi kenan sai in ba kowane ba
Amma tamkar ran tashe kai malam wasan ga ba zai kare ba wannan kasa
Wani yanki da ta'addaci su kai fice da su sha su ci har sui riga
Danyan mai na kasa ne du amma suf fasa bututu sui burga
Ba mai iya ce mussu a hir sai sulhu gyaran ya zama nag ganga
An gyara ba a gyara an yaga kidnapping su ne manya wannan kasa
In ka kalli batun wani kai tsam na rasshawa sai ka gane ashe comedy ne
In dai shari'a na kwazo su ka gane sai sui yi kifawar zaune
Sai su fadi suna shure-shure ba lafiya da yawansu iya shege ne
In wannan Nigeria ni na san ba mu gaji abin kunya ba wannan kasa
Kayan gwamnati namu ne in ka fasa ka sani mu kai wa cuta
Ba kishi mai za kai ne wa kasarka domin ka ga a inganta
In ka barnata lantarkinka ko titi ko ruwa wa zai alkinta
Wai gwamnati to kai ne ai duk dan kasa zai karrama al'ummarsa kishin kasa
Da za a ji tsoron Allah a sa kishi da dukka ba ai wayyo ba
Da za a rage ninanci da da rasshawa cin hanci a cire zamba
Da za a rike son juna ba ganda kwanmu ba zai tabe ba
Domin a yawa akwai mafita don tarin jama'ar nan alkhairi ne wannan kasa
Wane ne ba shi ne ba wannan kasa ban san wa zan dauka ba
In wannan Nigeria ce wannan kasa mamaki bai kare ba wannan kasa
In wannan Nigeria ce wannan kasa mamaki bai kare ba wannan kasa
In wannan Nigeria ce wannan kasa mamaki bai kare ba wannan kasa
In wannan Nigeria ce wannan kasa mamaki bai kare ba wannan kasa
Wane ne ba shi ne ba wannan kasa ban san wa zan dauka ba
In wannan Nigeria ce wannan kasa mamaki bai kare ba wannan kasa
Written by: Farfesan waka Sulaiman
instagramSharePathic_arrow_out

Loading...