Music Video
Music Video
Credits
PERFORMING ARTISTS
Ali Jita
Performer
COMPOSITION & LYRICS
Ali Jita
Songwriter
Lyrics
[Verse 1]
Eh, eh, eh, eh
Sallamata ga Jamila ta kasance
Yanzu mata ku taya ni addu'a ce
Don Jamila a cikin duhu hakan ce
Toh! tambarin kyau a gurinta ya kasance
Mu ci mai kyau manufar Jamila wacce
Ali jita ce yake kadawa
[Verse 2]
Jamila, gimbiya Jamila
Jamila, gimbiya Jamila
[Verse 3]
Jamila, gimbiya Jamila
Jamila, gimbiya Jamila
[Verse 4]
Sannu Jamila ki kwana lafiya eh
Addu'ata ki kara daukaka ne
Kin yi sa a da ke ake fadi ne
[Verse 5]
Kyau da kyauta halinki babu sai dai
Duka mata a gun ki su yaba dai
Sannu Jamila a bi ki ka'ida dai
[Verse 6]
Jamila, gimbiya Jamila
Jamila, gimbiya Jamila
[Verse 7]
Jamila, gimbiya Jamila to
Jamila, mai wayar salula
[Verse 8]
Farin idanu da tozali da kyalli
Jamila kenan mai murmushi da falli
Zaren aji ja Jamila duniyarki
Yawan masoya da masu tambayarki
Kina ta baccinki lafiya ta sa ki
Sannu Jamila Allah kare martabarki
[Verse 9]
Mai halin mammaki ina yaba ki
Mai ado da tsafta a gane ka'idarki
Mai shiga ta kaya kala-kala shirinki
Kina da gatanki babu mai taba ki
Jamila ke ce macen da an yaba ki
Sai a sa ki doki so o'e ko a jaki
Ki hau kilishi ki lankwashe kafarki
[Verse 10]
Ki zauna fada da ke da masu sonki
Shiga ta manya irin kalar sufarki
Ki sanya zinariya da zobunanki
Ki murmusa zuciya farin cikinki
Sai ki dubi Jita da kanta na fadinki
[Verse 11]
Jamila, gimbiya Jamila
Jamila, gimbiya Jamila
[Verse 12]
Jamila mai hakuri mai farin idanu
Jamila mai magana ce a sannu sannu
Jamila ko a dubun mata ba ki rainu
Gida idan babu Jamila ba ya zaunu
Kina da kimarki da martaba ta raino
Sunan Jamila a littafi ba ya konu
[Verse 13]
Jamila na fada Jita taya ni zance
Ko wa ta ja ki a gasa ta dauki rance
Allahu ya ba ki isarki daukaka ce
Magauta sun gan ki idon su ya makance
Taka da lafiya ribarki daukaka ce
[Verse 14]
To Jamila, gimbiya Jamila
Ah'ah, Jamila, gimbiya Jamila
[Verse 15]
Jamila, gimbiya Jamila
Jamila, gimbiya Jamila
[Verse 16]
Gidan Sarki ma akwai Jamila
Ko gidan gwamna ma akwai Jamila
Haka gidan malamai akwai Jamila
[Verse 17]
A gidan boka ba a yin Jamila
Ba a yin kauye in akwai Jamila
Babu wani birni wanda ba Jamila
Sha rubutu ga addu'a Jamila
Fassarar sunanki a ce Jamila
[Verse 18]
Haba! mace mai kyau ake nufi Jamila
Jamila, ah ah, Jamila
Jamila, haba haba, Jamila
Jamila, gimbiya Jamila
[Verse 19]
Jamila, gimbiya Jamila
Jamila, gimbiya Jamila
Written by: Ali Isah Jita


