Music Video

Music Video

Credits

PERFORMING ARTISTS
Ali Jita
Ali Jita
Performer
COMPOSITION & LYRICS
Ali Jita
Ali Jita
Songwriter

Lyrics

[Verse 1]
A sha ruwa
A sha ruwa
[Verse 2]
A marmatso, a marmatso, a marmatso
A marmasto masoya
A marmatso, a marmatso, a marmatso
A marmasto masoya
A rairaya, a rairaya, a rairaya
A rairaya 'yan mata
[Verse 3]
Soyayya ruwan zuma ce
Soyayya ruwan zuma ce
Kiyayya ruwan guba ce
[Verse 4]
Ya Jallah Wahidun Ya Allah kawo da mai biya na
Jallah Wahidun Ya Allahu kawo da mai biya na
[Verse 5]
Tamburan masoya nake a yau saboda so da kauna
Fata nake masoya a rayuwa lafiya su zauna
Su taimakawa junansu kar su bar Iblis ya zauna
[Verse 6]
Soyayya ruwan zuma
Soyayya ruwan zuma
Ashe kiyayya ruwan guba ce
[Verse 7]
Ga tambarin masoya
Ga tambarin masoya
[Verse 8]
Ranar zuwan amarya wannan ranar farin ciki ce
Ina kiranku mata rawar biki kun ga ka'ida ce
Mu juya mu rausaya
Baya mu waiwaya
[Verse 9]
Jita tana biya na
Kowa ya zagaya
In dai da so da kauna
Sai kun faranta rai na
Sai kun yaba wa juna
[Verse 10]
A rausaya masoya
A girgiza masoya
[Verse 11]
A marmatso, a marmatso, a marmatso
A marmasto masoya
A marmatso, a marmatso, a marmatso
A marmasto masoya
A rairaya, a rairaya, a rairaya
A rairaya 'yan mata
[Verse 12]
Kowa ta zo ta motsa domin juyinta ka'ida ne
In dai ta ja baya mu a gurinmu mai bakin ciki ce
Soyayya ashe zuma ce
Mai yin ta ya yi dace
Kauna ko nasara ce
Hadin naku daukaka ce
Ki bi shi ka'ida ce
Ya so ki ya amince
Kin so shi kin amince
Abokiyar zaman ce
Da ke kin ga aya amince
[Verse 13]
Yana da kyau amarya ko da abinci ku ci a tare
Yana da kyau amarya a share daki dakin amare
Yana da kyau amarya wanka kullum ki sa turare
Mai kamshi gidan amare
Komai a nai a tsare
Zance kuke a tare
Junanku babu ware
Kun hadu babu ware
Zauna gidanki more
Komai yai miki daure
[Verse 14]
Ba cuta yake nufi ba
Ba kya sha bakin ciki ba
Ba zai bata ranki ne ba
Aure ba fada ba ne ba
Mata ba diya ba ce ba
Abokin zama ku duba
In ya shigo ki tarba
[Verse 15]
A rausaya masoya
A rausaya masoya
A girgiza masoya
[Verse 16]
Wakar gidan amare
Waka nake tabawa
Ali Jita ina tabawa
[Verse 17]
Soyayya ruwan zuma
Soyayya ruwan zuma
Ashe kiyayya ruwan guba ce
Soyayya ruwan zuma ce
In ka sha sai ka ba masoyi
[Verse 18]
Allahu ya nufa auren nan waye yake hanawa
Yau ya zamo mijin aurenki komai yake tarewa
Abinci magani, da ruwan shanki duk yana ajewa
Sam babu ran ajewa
Ko daren daren dadewa
Arziki ana dadawa
Kowa yana yabawa
Soyayya ana dadawa
Don ke yake ta zo wa
Don shi kike fitowa
[Verse 19]
A rausaya masoya
A girgiza masoya
[Verse 20]
A marmatso, a marmatso, a marmatso
A marmasto masoya
A marmatso, a marmatso, a marmatso
A marmasto masoya
[Verse 21]
Ya Jallah wahidun Ya Allahu kawo da mai biya na
Jallah wahidun Ya Allahu kawo da mai biya na
Allah ka ba wa wanda yake ba mu don ba ka hana ba
Kauna tana da rana mun gan ta ba kadan ba ne ba
Mai kin ka kar ka yarda da zancensa ba hakan ba ne ba
[Verse 22]
Ban san bakin ciki ba
Ban san da yaudara ba
Ban daina addu'a ba
Ban daina daukaka ba
Ba boka yake yi min ba
Tsafi fa ban iya ba
Ban san ma ta ya ake ba
[Verse 23]
Nai dogaro ga rabba
Karyarku masu zamba
Ni ba rago ba ne ba
Ban raina mai kira ba
Nai godiya masoya
[Verse 24]
Soyayya gami da kauna
Allah ka ba wa wanda yake ba mu duniya ya mora
Soyayya ruwan zuma
Soyayya ruwan zuma
Ashe kiyayya ruwan guba ce
[Verse 25]
Zancen ga mai dadewa
Zance na ke tabawa
Toh ina masoya
[Verse 26]
A rausaya masoya
Yara ina masoya
Mata kuna ina
Yara kuna ina
Iyaye kuna ina
Kanne kuna ina
[Verse 27]
A rausaya masoya
Ruwa kala-kala ne
Akwai ruwa na kogi
Akwai ruwa na rafi
Akwai ruwa na randa
Akwai ruwan madaci
Akwai ruwan zuma ma
[Verse 28]
Soyayya ruwan zuma
Soyayya ruwan zuma
Ashe kiyayya ruwan guba ce
Written by: Ali Isah Jita
instagramSharePathic_arrow_out

Loading...