Credits

PERFORMING ARTISTS
Ali Jita
Ali Jita
Performer
COMPOSITION & LYRICS
Ali Jita
Ali Jita
Songwriter
Palaspa Chan Changi
Palaspa Chan Changi
Songwriter
Prince Prince Prince
Prince Prince Prince
Songwriter
PRODUCTION & ENGINEERING
Prince Prince Prince
Prince Prince Prince
Producer

Lyrics

Damina ba ƙarewa, to Allah Ya yarda
Prince Production
Ga zakin nan, zaki ba kure ba
Ga zakin nan, zaki ba taure ba
Aikin da wuya yaro ba a soma ba
Kun gane maza ko da ba a duba ba
Har yau nine, ba a samo sauyi ba
Balle in ce in zauna in huta ma
Har yau kan dai, ga gangan ba a kwace ba
Zaki dauri, har bana ma ba a sauya ba
Na kama zarena har yau bai tsinke ba
Na iya allo, yaya ba zan wanke ba
Lamarin Zaki, ai daga Allah ne Rabba
Ƙaryar dodo, ciji bai motsa ba
Na zaga dare, tarkon bai kama ba
Mai gurnani, ba zai taɓa raki ba
Ga jiki da jini, ba a kwana da yunwa ba
Tashin ƙura tai sama wannan zaki ne
Ƙarfi ga lafiya
Mun saba gwagwarmaya
Daga ji ba tambaya
A gari ko tsangaya
Wanne ne za a yi wanne ne ba za a yi ba
Abin nema ƙauna, abin guzuri ƙauna
Ban iya zagi ba, ba a zagi na
Ban iya reni ba, ba a rena ni
Ban san cuta ba, domin ba a koyan ba
Ni ba ɗan wawa ba, ba mai zubda mutunci ba
In ka zagen ka zaga, ba lallai in rama ba
Domin in kun lura, ban fiye sakarci ba
Aikin da wuyar koyo, yaro bai saba ba
Ai nima ban saba ba
Sai dai na rike waƙata kuma waƙar ta riƙe aiki na
So and so (Soyayya)
So and so (Soyayya)
Kiɗan soyayya ne, ruwan zuma mai ƙarewa
Ban san soyayya ba, ruwan zuma kan ƙareta
Sai ran da na ƙullata, kwanaki kaɗan ta lalace
Mutunci harka ce, soyayya ma harka ce
Gaba ɗaya babu kamar ƙauna
Don mutunci na lura, ana iya saidawa
Soyayya ma na lura
Tana iya ƙarewa ƙauna ko ba ta ƙarewa
Kuma ƙauna ba a saidawa
To kiɗan soyayya ne, ruwan zuma mai ƙarewa
Abin nema ƙauna, abin guzuri ƙauna
Allah kawo ƙauna, ƙauna ba don duka ba
Kuma ƙauna ba don zagi ba
So and so (Soyayya)
So and so (Soyayya)
(Mu sha ruwa domin sabo) Soyayya
Sha ruwa domin sabo
Ba don yunwa ba
Ba don yunwa ba
Written by: Ali Isah Jita, Palaspa Chan Changi, Prince Prince Prince
instagramSharePathic_arrow_out

Loading...