album cover
Fana'e
703
Afro-Beat
Fana'e was released on October 10, 2022 by Sadiq Saleh Prod. Distri. By Mr. ArewaBlog as a part of the album So Kenan
album cover
Release DateOctober 10, 2022
LabelSadiq Saleh Prod. Distri. By Mr. ArewaBlog
Melodicness
Acousticness
Valence
Danceability
Energy
BPM119

Credits

COMPOSITION & LYRICS
Sadiq Saleh
Sadiq Saleh
Songwriter

Lyrics

[Chorus]
Akwai lamarin da ke ta caza min ni ruhi
Da na kalle ki sai na ƙara shiga fana'i
Ni ma akwai lamarin da ke ta caza min ni ruhi
Da na kalle ka sai na ƙara shiga fana'i
[Verse 1]
Ku tayi ni da murna nai dace
Wacce na so ta kamar na susuce
Ta ba ni son ta gare ni nasara ce
Oh, Allah ya ba ni ke
Ba za ni shalleke
Cikin su ni daban
Wanda ya samo kamar ki ya ɗara kowa
[Verse 2]
Abadan da'iman da son ka ni za na margaya
Ka ratsa can cikin jinin jiki har da zuciya
Ina farin ciki in ka kira ni da masoyiya
Ce habibiya rai da zuciya
Mallakinka ce
Ni ko da za a mai da ni gawa
[Verse 3]
Zo mu zauna kamar mu saɓa ne
Mai cin amana wani ko mugu ne
Mai ginin sanda faɗin wanzan ne
Hannu ki riƙe
Ban so ki sake
Tudu mu haye
Tudun nasara mu iske rabo
[Verse 4]
Duba da hankali cikinsu ma kai fa kai daban
Gwara mu wataya a birnin so, son ka sai ka ban
In barka la-la
Sai mutuwa ta yi ajalin
Kai ɗaya ne a rai
Zan rayu ni da kai
Ka cika cokalin chin nasara naka-naka ne ƙauna
[Verse 5]
Ƙaunarki baɗini yau ma an gan shi zahiri
Ni ma ki mi ni so tamkar mama da jinjiri
Matso-matso kiji
Ga wani saƙo da shiʼiri
A ya ƙudiri ga albishiri
Da ke zana yo aure, aure sunnar ma'aiki
[Verse 6]
Ni dai ka biya ni tun da ka cika alƙawari
Saura ɗan kaɗan da ni da kai ai ayyiyiri
Rana an saka mana maƙiya kun ga zahiri
Haushi ya kashe ku
Kun wahalar da kanku
Kun yi ƙashin wuya
Kun kasa bacci ga shi muna ta farin ciki
Oh-oh-oh-oh
[Chorus]
Akwai lamarin da ke ta caza min ni ruhi
Da na kalle ki sai na ƙara shiga fana'i
Ni ma da akwai lamarin da ke ta caza min ni ruhi
Da na kalle ka sai na ƙara shiga fana'i
[Outro]
It's prince on the mix
Written by: Sadiq Saleh
instagramSharePathic_arrow_out􀆄 copy􀐅􀋲

Loading...