歌詞

Karshen furuci na dake kiyi hakuri Bar batu na so ni dake ba aure Karshen furucin ka babu dadin sauraro Kayi min afuwa in nayi ma laifi ne in sani Soyayyar ka ta kama dukkan jiki na Ban jin zan rayu idan ba kai a guri na Karshen furuci, kayi raina na kuna In laifi nayi ma sai nace kayi hakuri Laifin baki yi min ba yanmata bar kuka Son ki na cikin zuciya ta ba shakka Mahaifin ki ya cutar dani ya sani kuka Bani mantuwa dashi ya sani a rana Mata ta dana ke auren sunnah Yazo yace ita yake so da kauna Wai sai in sake ta ya aura mata guna Ni ko nace naki na bada muradi na Ya nuna karfi da mulkin sa guri na Na sake ta ya aura haka ban so ba Karshen furucin ka babu dadin sauraro Kayi min afuwa in nayi ma laifi ne in sani Karshen furuci na dake kiyi hakuri Bar batu na so ni dake ba aure Laifi na mahaifi na kar da ka shafa min Zaki na zumar soyayya ka dandana min In ka guje ya zanyi masoyi ni tausaya min In har na rasa ka na rasa muradi na Karshen furuci na dake kiyi hakuri Bar batu na so ni dake ba aure Kayi hakuri masoyi ka ceci rai na Kiyi hakuri kin ji karshen furuci na In ka kini ya zanyi, ina zan sa kai na? Kiyi hakuri ni da ke ba aure
Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out